Connect with us

LABARAI

Assasa Zaurukan Sulhu A Bauchi Ya Taimaka Wajen Gyaran Tarbiyya – Adamu Ningi

Published

on


An bayyana assasa zaurukan sulhu don magance kalubalen da ake fiskata game da matsalar lalacewar tarbiyyar mutane a unguwanni a matsayin babbar hanyar da take tallafawa wajen rage rigingimu a tsakanin jama’a tare da rage ziyartar kotuna ko ofisoshin ‘yan sanda a lokacin da aka samu rashin jituwa a tsakanin jama’a.

Alhaji Adamu Hashimu Ningi Sakataren Zauren sulhu da tarbiyyar al’umma na unguwar ma’aikatan jinya da ma’aikatan hukumar ruwa da na ma’aikatar ayyuka da ke Bauchi shi ne ya bayyana haka cikin hirar sa da wakilin mu a Bauchi inda ya kara da cewa; sun kai shekara biyu suna kokari don assasa zauren sulhu saboda inganta rayuwar su da ta yaran su da ta jikoki da kanne kamar yadda sauran unguwanni suka yi, saboda sun jima suna wani abu kamar don ganin an samu ci gaban tarbiyya a unguwannin. Musamman ganin yadda ake ciki a yanzu wasu za su iya ganin an yi haka don a kuntata musu don an ce gyara kayanka bai zamo sauke mu raba ba. Amma idan aka jima kowa zai ga fa’idar abin da suka yi wajen gyaran tarbiyyar mutane musamman a wannan lokaci da suka hada da gwamnati suka shigo da hukumar shari’a cikin lamarin aka bi kundinta kuma ta kaddamar kamar yadda aka yi a wasu unguwanni. Don haka idan an ga fa’idar lamarin wasu unguwannin suma za su bi sahu su yi hakan.

Adamu Hashimu bayyana cewa tun farko sun fara tsare tsare don tare wasu lamurra a unguwar da ke faruwa inda suka yi kwamitoci dabam dabam wanda suka shafi na tarbiyya da na tsabtar muhalli da kwamitin lura da marayu da kwamitin lura da ilmi da masallaci da kwamitin tsaro da kwamitin hana yara wasa a masallaci da kwamitin gyaran tarbiyya da tsara yadda samari da ‘yan mata ke hira da sauran su. Musamman kowane batu ya taso kan lamarin ake turawa kwamitin da ya dace, idan ya gagare su sai su tura wa babban kwamiti na shugabannin unguwa sai su zauna, idan lamarin ya faskara sai a tura zuwa hukumar shari’a ta Jihar Bauchi idan suma ya fi karfin sai su tura zuwa kotu.

Don haka ya bayyana cewa irin wadannan kwamitoci suna rage rigingimu a cikin al’umma inda ake samun saukin zuwa kotu ko ofisoshin ‘yan sanda a na kashe kudi ko daukar lauya kan abin da bai taka kara ya karya ba wanda za a iya sasantawa a zauna lafiya a cikin unguwa, wanda ke da gaskiya a bashi gaskiya wanda ya yi kuskure a nuna masa domin ya gyara a ci gaban da zaman tare lafiya.

Shi ma shugaban zauren sulhu na unguwannin uku Dokta Sadik Garba Abubakar wanda malamin jami’a ne ya bayyana cewa kwamitin ya kunshi unguwanni uku na ma’aikatan jinya saboda akwai abubuwa da ke faruwa tsakanin matasa wanda ke tayar musu da hankali yadda suke shaye-shaye da aikata ayyuka na laifi ko sace sace.

Don haka suka kirkiro kwamitoci sha daya da kuma wasu kwamitoci guda bakwai da ke tsara lamurran unguwar ta yadda kowa ke gamsuwa game da yadda ake gudanar da sha’anin gyaran tarbiyya a wadannan unguwanni.

Dokta Sadik Garba ya bayyana cewa wannan aiki ne da addini ya amince da shi wanda ya dauki shawarar su shi ne zai amfana don a gyara zamantakewa kamar yadda kowa ke son ganin iyalan sa sun kasance mutanen kirki musamman a irin wadannan unguwanni da ke makobtakar unguwar sheke aya ta bayan gari da babbar tashar mota da kasuwar muda Lawal da ke Bauchi. Don haka ya ja hankalin mazauna wadannan unguwanni da su bayar da hadin kai wa kwamitocin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai