Connect with us

LABARAI

An Bude Masallacin Markaz Ikira’a A Kano

Published

on


 

A wannan Juma’ar ne ta biyu ga watan Ramadan mai alfarma aka yi bikin bude Masallacin Masjid Markaz Ikira’a Al- islamiy a Unguwar Kwanar Dawaki da ke Karamar Hukumar Dawakin Kudu a Jahar Kano.

Masallacin wanda ya kunshi Masallacci da makaranta da kuma cibiyar Horar da Matasa da sauran al’umma Ilimin Addinin Musulunci da karatun alkur’ani mai girma da kuma Dakin tarurruka kamar taron karawa juna sani da makamantansu duk a wannan Masallaci na Masjidul Markaz Ikira’a Al-islamiy a karkashin Jagorancin Limamin Masallacin Dr. Abdulmutallib Ahmad Muhammad a wannan rana

Kuma jagoran masallacin da kuma cibiyar da ke wannan Masallaci ya bayyana farin cikinsa da irin wannan cigaba yanki ya samu na samun Masallacin Juma’a da makaranta da kuma wannan cibiya da zata taimakawa al’umma wajan samun ilimi da wayewa. Kasancewar wannan cibiya da akayimata rigista dan aikinta yasamu Nasara.

Shi ma Babban Bako mai Jawabi Sheikh Abdulwahab Abdullah kira yayi ga Mawadata da suyi amfani da damar da Allah ya ba su wajan gina alkairi da tallafawa Matalauta Talakawa musamman a watan na Ramadan domin fidda Mabukata daga cikin kunci na rayuwa inda kuma ya yi Nasiha da Shugabanni akan rukon Amana da Adalci inda ya sake nanata kira da Nasiha ga Iyaye wajan kula da sharrin da ke cikin kafofin sadarwa na zamani musamman irin social media a Yau da suke lalata Tarbiyar Matasa Maza da Mata musamman bangaren nuna tsaraici da rashin kunya kasan cewar ya’ya Amana ne a gurin Iyaye.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai