Connect with us

LABARAI

Majalisa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 15 Don Titin Bauchi Zuwa Kano

Published

on


A  Larabar nan ne Majalisar Zastarwa ta gwamnatin Nijeriya ta amince da fitar da tsabar kudi har Naira biliyan goma sha biyar da miliyan dari hudu da hamsin da hudu (N15.454 billion) domin samun nasarar  shimfida titi mai nisan kilomita 58.9 a tagwayen hanyoyin na Magami zuwa Kwajali zuwa Lingi, titin wanda ya hade zuwa Bauchi da jihar Kano.

Bayan nan kuma Majalisar ta amince da fitar da kudin domin shimfida titin Abuja zuwa Keffi zuwa Akwanga zuwa Legas zuwa titin Makurdi.

Ministan Wuta, Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, shi ne ya shaida hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala ganawarsu da majalisar zastawar Nijeriya wadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ya ce, “Ina son na yi bayani kan cewar a wannan babin, wani kilomita 16 a babban titin Legas za a gudanar, sannan kuma wani titi mai nisan kilomita 251.7 wanda ya kunshi hanyoyi tara daga Otukpo zuwa Makurdi, dukkanin kilomitan sun kai 268.5 duk mun amince za a yi su a kan tsabar kudi Dala 995,004.95,” Kamar yadda ya shaida.

Ya ci gaba da cewa, “Hanyar Abuja zuwa Keffi wanda aka amince da yinta a 2015 yanzu haka kudin wannan aikin ya fito,” In ji Babatunde.

 


Advertisement
Click to comment

labarai