Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Daure Tsohon Gwamnan Filato Jang A Gidan Yari

Published

on


Tsohon Gwamnan Jihar Filato Jonah Dabid Jang a shekaran jiya ne ya ci gaba da kasancewa a gidan wakafi, biyo bayan kin amincewa da bayar da belinsa da Alkalin babban kotun Jos Justice Daniel Longji ya yi.

Jang zai ci gaba da kasancewa a gidan yarin har zuwa ranar 24 ga watan Mayun nan da muke ciki.

Jonah Dabid Jang an gurfanar da shi ne a gaban kotu kan laifuka dai-dai har guda 12 da ake zargisa da aikatawa wadanda dukkaninsu sun shafi cin hanci da rashawa na tsabar kudi har Biliyan N6.3 wadanda ya karkatar da su zuwa lalitarsa daf da barinsa ofis a matsayin gwamnan jihar.

A cikin tuhumar, an kuma hada da jami’in da ke kula da hidimar fitar da kudi na ofishin Sakataren gwamnatin jihar Filato Yusuf Gyang Pam, a bisa zargisa shi ma da wawushe naira miliyan N11.

Haka kuma, lauyan kariya na tsohon gwamnan, Barista Robert Clarke, ya rubuta bukatar bayar da belin Jang a ranar Litinin.

Clarke ya bayyana cewar Jang ya kamata ya samu ‘yanci domin a samu zarafin gudanar da bincike, ya bayyana cewar a bisa doka babu yadda za a yi a hukunta Jang har sai an tabbatar da zargin da ake yi a kansa tun da a yanzu a matakin tuma ake.

Haka shi kuma a ta fanninsa, Lauyan hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa EFCC, Barista Rotimi Jacob (SAN), ya nemi kotun ta gaggauta yin fatali da bukatar bayar da belin tsohon gwamnan da aka shigar mata, ya bayyana cewar idan aka yi la’akari da irin muhimman zarge-zargen da suke kan wanda suke kara.

Ya ci gaba da bayanin yadda Jang ya wawushi dukiyar jiharsa “A tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun shekara ta 2015, wanda muke zargi na farko ya amshi kudi har naira biliyan hudu (N4billion) daga kudin jihar. Sannan kuma bankin kasa (CBN) ta bayar da naira biliyan biyu (N2 billion) domin samar wa mutanen Filato aiyukan yi, gwamnan ya wawushe kuma yanzu a nemi sakesa ta hanyar beli ya tafi gida ya ci gaba da harkokinsa kamar kowani tsarkakekke, ba mu gamsu ba,” In ji Lauyar EFCC.

Sai dai kuma Alkalin Kotun, Justice Daniel Longji ya dage ci gaba da saurakokin karar har zuwa ranar Alhamis 24 ga watan Mayu domin ci gaba da tattauna kan bukatar bayar da belin Jang.

Sanatan da ke wakitar Filato ta Arewa kuma tsohon gwamnan jihar Filato, ya iso harabar kotun ne da misalin karfe 9:28 na safiyar ranar, a dikin mota 15-seater Toyota Hiace wacce aka saukesa hade da rakiyar EFCC da kuma ‘yan sanda.

Masoya da magoya bayan tsohon gwamnan Filaton sun yi ta zanga-zanga suna masu cewar ya kamata a yi masa adalci.

Kawo yanzu dai Jonah Jang na karkame a gidan yari kan zarge-zargen rashawa da wawushe dukiyar jiharsa gabanin ficewarsa daga ofishin gwamnan jihar a 2015.

 


Advertisement
Click to comment

labarai