Connect with us

LABARAI

Gwamnan Bauchi Ya Nada Sabbin Sakatarorin Dindindin 18

Published

on


Gwamnan Jihar Bauchi, Lauya Muhammad Abdullahi Abubakar ya amince da nada sabbin Sakatarorin Dindindin (Permanent Secretaries) guda goma sha takwas (18) domin kyautata aikin gwamnati a jihar.

Wannan bayanin na cikin wata sanarwar manema labaru ne wacce shugaban ma’aikatan Bauchi Alhaji Liman Bello ya raba dauke da sanya hanun Yusufu M. Karamba wacce aka raba wa manema labaru a jiya.

Sanarwar ta bayyana cewar daga ranar 18 na watan Mayu 2018 ne nadin nasu ya fara aiki nan take, sanarwar ta yi bayanin cewar an bi cancanta da kuma dacewa hade da duba kwazon kowa gabanin amincewa da nadasa ko ita a matsayin sakataren dindindin a jihar.

LEADERSHIP A Yau, Asabar ta nakalto jerin sunayen sabbin Sakatarorin dindindin da jihar Bauchi ta samu, sunayen gasu kamar haka: Shehu Aliyu daga karamar hukumar Dass, Dawud M. Mohammad Yakubu Bauchi, Maijama’a Mohammed Dewu daga Kirfi, Hauwa Yelwa Abubakar daga karamar hukumar Bauchi, Aliyu Babayo daga Gamawa, Kabiru A. Sade daga Darazo, Dakta Yahaya Yarima Misau, Umar Shehu daga karamar hukumar Tafawa Balewa.

Sauran sabbin Sakatarorin Dindindin din da gwamnan ya hada su ne  Hamisu Hassan Mohammed daga Toro, Lydia Haruna Tsammani daga Bogoro, Abdulhamid Moh’d Jibrin daga karamar hukumar Giade.

Haka kuma gwamnan ya nada Hajiya Jummai Liman Bello daga karamar hukumar Katagum (shugaban gidan rediyon Bauchi a halin yanzu) a matsayin sabowar sakataren dindindin, dauran karashin dai sune Magaji A. Dawuwa shi ma daga Katagum, Adamu Hashimu daga Warji, sai kuma Injiniya Stephen Abubakar daga Dass.

Karashin sabbin wadanda gwamnan M.A ya nada sun hada da Lydia J. Shehu daga Alkaleri, Moh’d Danlami Garba daga Gamawa sai cikon na 18 din a jerin wadanda gwamnan ya nada mai suna Barista Buhari A. Disina.

Sanarwar ta shugaban ma’aikatan jihar Bauchi Alhaji Liman Bello ta ci gaba da bayanin cewar wannan nadin an yi ne a bisa cancanta ba tare da bin son rai ko kuma wani fifiko ba, “Dukkanin wadannan nade-nade ya biyo bayan amincewa da irin kwazon kowani daya daga cikin wadanda suka samu nadin ne. haka kuma, nadin na daga cikin manufar inganta aikin gwamnati a jihar ta Bauchi,” In ji Bello.

Liman Bello ya bayyana cewar wannan nade-naden zai fara aiki ne nan take.

 


Advertisement
Click to comment

labarai