Connect with us

LABARAI

Fitowar Mustapha Takara Ta Girgiza Gwamnatin Jigawa

Published

on


Fitowar Mustapha Sule Lamido datakarar majalisa daga mazabar jigawa ta tsakiya a karkashin tutar jam’iyyar PDP al’amari ne da ya girgiza gwamnatin jihar Jigawa, saboda irin dimbin magoya bayan da ake ganin yake da su.

Wannan kalami ya fito ne daga bakin daya daga cikin makusantansa, Alhaji Hasssan Birnin kudu, wanda kuma da shi ake zagaya wajen kamfen na neman kuri’ar samun nasara donmin Mustaphan ya zama dan majalisa.

Alhaji Hassan ya shaida wa wakilinmu cewa, duk inda suka zaga jama’a ke bumbunto wa suna nuna goyon bayansu ga wannan dan takara nasu kamar yadda ya ce.

Da yake karin haske kan sirrin wanna goyon baya da ya ce dan takarar nasu na samu, cewa ya yi duk da cewa, Mustapha yaro ne a shekaru, ammam kuma dattijo ne a tunani, domin yana yin abubuwa irin na dattijantaka.

Wannan babban al’amari ne da  Hassan ya bayyana a matsayin abin da ya kawo wa dan takarar na su farin jini, sannan kuma mutum ne mai taimaka wa a l’umma da ya dade yana yin hakan. Tun kafin Mustapha ya san zai tsaya takara yaro ne wanda yake da tausayi, saboda haka dukkan matsalar da aka zo masa da ita wadda ke bukatar taimakon yakan yi iya kokarinsa wajen ganin ya taimaka.

Sannan kuma wani abu da al’ummar wannan mazaba da Mustapha ya fito ke neman canji shi ne yadda wanda suka zaba a matsayin dan majalisa ba ya ko zuwa gida ballantana ya ji matsalolin jama’arsa ya kuma samu su tattauna yadda za a samu mafita.

Haka kuma Hassan ya ci gaba da cewa, babban abin da ke kara karfafaf musu gwiwa wajen ci gaba da goyon bayan Mustapha a matsayin wanda suke so za su zaba a matsayin dan majalisarsu shi ne, yadda ya rungumi dakkan al’ummar yankinsu ba tare da nuna wani bambanci ba.

Wani abu da mutanen Mustapha ke alfari da shi, ko  ba komai gidansu gida ne da ya yi fice a siyasar akida, kamar yadda kowa ya san mahaifinsa Alhaji Sule Lamido da tsayuwa a kan kaifi daya,

Saboda haka  Hassan ya ci gaba da cewa, kasancewar Sule lamido mutum ne da ake girmamamawa a siyasar jihar Jigawa ya sa shi Mustapha ya samun wannan albarkacin in da duk inda ya zaga  mutane na kallonsa a matsayin wanda ake fatan ya gaji mahaifin domin kuwa kamar yadda mutanen suke  cewa, ba samu wani gwamna a jihar jigawa day a yi aikin raya kasa da ci gaban al’umma ba kamar Sule Lamido ba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai