Connect with us

LABARAI

An Nuna Wa Matasa Illar Shan Miyagun Kwayoyi

Published

on


Uwar gidan gwamnan jihar Katsina Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari, ta bayyana cewar iyayen yara matasa maza da mata musamman iyayen da suka san  ‘ya’yansu na shan miyagun kwayoyi a jihar Katsina da ma sauran jihohin Nijeriya baki daya da su tsawata wa ‘ya’yansu game da shan miyagun kwayoyi.

Uwargidan ta yi wannan tsokaci ne a Kwalejin ’yan mata da ke garin Funtuwa. Yayin da take gudanar da jawabinta a wajen taron tsawata wa da nuna wa matasa illar  shan miyagun kwayoyi Hajiya Hadiza, ta ci gaba da cewa, wajibi ne iyayen yara matasa maza da mata su sanya wa ‘ya’yansu ido game da abokan da suke ma’amala da su domin kauce wa lalatattun abokai  wadanda ke shan miyagun kwayoyi. Sannan kuma ta umarci al’ummar jihar Katsina da Nijeriya baki daya da su hada karfi da karfe domin yakar ko kashe wadannan al’amari mai cutar da matasa. Shi dai wannan taron gwamnatin jihar Katsina ta kirkiro shi, domin samun nasarar kashe wannan al’amari na shan miyagun kwayoyi.

Taron ya kunshi dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro na jihar Katsina irin su, kwamishinan ‘yan sanda  Muhammed Wakili da tawagarsa, jami’an hukumar kiyaye hadura da jami’an tsaro na farin kaya da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da ‘yan sintiri da cibil defense da iyayan kasa hakimai da magaddai masu hannu da shuni da sauran al’umma.

Kadan daga cikin manyan baki a wajan taron sun hada da Dakta Bishir Ruwan Godiya da shugabar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi Hajiya Maryam wadda ta samu wakilcin Alhaji Mustapha Mai Kudi da shugaban kwamitin da’awa Malam Aminu Daurawa Kano da sauran su.

A nata jawabin shugabar hana sha da fatauncin miyagun kwayoyi Hajiya Maryam ta roki al’ummar jihar Katsina a duk wata kwana ko sako ko wani gurin da ba a san kome ake saidawa a gurin  ba, da su gaggauta shaida wa ofishin ‘yan sanda  ko ofishin N.D.L.A.  haka kuma ta ci gaba da rokon gwamnatin jihar Katsina da ta taimaka ta sake masu kayan aiki na zamani kamar motoci da sauran abubuwan da za su taimaka gaya a wurin aikinsu ya tafi daidai.

Shi ma a nasa jawabin Dacta Bashir ruwangodiya cewa ya yi kamata ya yi a fadada irin wannan taro daga jiha zuwa kananan hukumomi  su ma su rinka irin wannan taro shi kuma shugaban kwamitin da’awa na jihar Kano Malam Aminu Daurawa cewa ya yi a kirkiro wani abu na taimako  ga duk wanda ya ce ya daina shan miyagun kwayoyi za a yi masa muhimin abu wanda hakan jihar Kano ta yi, ta samu nasarar wannan al’amari. Sarkin Maskan Katsina hakimin Funtuwa Sambo Idris Sambo  ya shawarci matasa ne da su daina irin wadannan shaye-shaye domin su yi rayuwa cikin mutuncisu da samun zuri’a ta gari.  Sai shugaban riko na karamar hukumar funtuwa Abdullahi Abubukar Kutawa  yabawa ya yi  da kyayawan shirin da gwamnatin jihar Katsina ke yi na kashe miyagun abubuwa irin wadannan wanda zai taimaki kasa da al’ummar kasa baki daya, sannan kuma matasa su zama mutane nagari.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai