Connect with us

LABARAI

Zabukan APC A Yobe: Wasu Kososhin Jam’iyya Sun Yi Barazanar Zuwa Kotu

Published

on


Wasu daga cikin kososhin jam’iyyar APC a jihar Yobe sun yi barazanar zuwa kotu matukar uwar jam’iyya a jihar ba ta dubi korafin rashin adalcin da suke zargin an nuna musu a zabukan shugabanin unguwanni da kananan hukumomin da ya gudana a jihar.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin, Alhaji Adamu Yaro, a zantawar sa da manema labarai, ranar Lahadi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, wanda ya fara da bayyana cewa bisa lura da yadda aka gudanar da wadannan zabuka a jihar Yobe, ya saba ka’ida tare da yiwa dokoki karan-tsaye wanda kuma yana iya yiwa babban zabe mai zuwa tarnaki ga jam’iyyar.

“zabuka ne wadanda a karara suke cike da rashin adalci, wadanda kuma idan ba a dauki matakin gyara ba, zai sanya dole mu tunkare shi da duk karfin mu a gaban kuliya”.

“a matakin jam’iyya, kuma a matakin gargadi, dole a dauki kwakkwaran matakan gyara tare da hada kan yan jam’iyya domin dinke barakar cikin gida, wannan domin kaucewa sabatta-juye tare da maida wasu yayan bora da ya jefa wasu jam’iyyu da dama shiga cikin halin kaka nikayi a baya”.

Bugu da kari kuma, ya bayyana cewa da dama daga cikin masu sha’awar tsayawa takara a makamai daban-daban, wadanda tuni sun sayi fam din takarar da jam’iyyar ta tsara tare da lambar asusun bankin da masu sha’awar za su biya da mika shi a sakatariyar jam’iyyar.

“wanda a karshe kuma, wanda kuma da dama daga cikin wadanda suka sayi fam din sun dawo dashi- amma kuma sai aka buge da tsarin goyon baya ba zabe ba, wannan yiwa kundin tsarin jam’iyya karan-tsaye ne da saba ka’idojin gudanar da zabukan shugabanin jam’iyya wanda kuma ba zamu taba lamunta da shi ba”.

“yana da kyau a fahimci cewa lokacin sasanta wa ko doki-dora ya wuce, saboda wannan muna kira ne kan dole a rusa wannan zaben tare da gudanar da sabo fil, mai cike da gaskiya da yanci”. Inji kososhin jam’iyyar.

Har wala yau kuma, jiga-jigan jam’iyyar sun bukaci uwar jam’iyya a jihar Yobe da su ayyana zabukan unguwanin tare da na kananan hukumomin da aka gudanar a jihar a matsayin rusashe.

“kuma jam’iyyar APC ta kuduri aniyar sake gudanar da wani sabon zabe, ta baiwa duk wanda ya mallaki fam din damar shiga zaben- cikin yanci da adalci”. Ya nanata.

Da yake mayar da martani dangane da wadannan zarge-zargen, sakataren jam’iyyar APC a jihar Yobe, Alhaji Abubakar Bakabe, ya shaida wa manema labarai cewa jam’iyyar APC a jihar Yobe ta cimma matsaya a kan wannan tsarin da ta gudanar a matakin unguwani da kananan hukumomi, kuma wannan ya faru ne ta dalilin karancin lokacin da aka dashi da kudaden da za a gudanar da zabukan.

“wannan wata yarjejeniya ce wadda jam’iyya ta cimma matsaya a kan ta, kan a sake goya baya ga wadanda suke a kai tare da maye gurbin wadanda Allah ya yiwa rasuwa ko suka canja da wadanda suka kaura daga jiha; wannan shi ne tsarin da muka yi matsaya a kai kuma muka aiwatar”. Inji shi.

Da yake bayar da jawabi dangane da zargin dakile aniyar wasu masu sha’awar takara, baya ga har sun riga sun sayi fam, sai ya ce “gaskiya ni ban ga ko mutum daya wanda ya zo sayen fam din ba, ballantana ma har ace an hana shi ba”.

A hannu guda kuma, Alhaji Mohammed Lamin, daya daga cikin jigogin jam’iyyar kuma kwamishinan ilimi a jihar Yobe, ya bayyana cewa suna sane da wannan dambarwar, mai cike da korafe-korafe kala-kala, tattare da yadda aka gudanar da wadannan zabukan. Wanda kuma ya bayyana da cewa”wadannan matsaloli ne na cikin gida, kuma Insha Allah zamu warware su cikin tsanaki”.

 


Advertisement
Click to comment

labarai