Connect with us

LABARAI

Hukumar Kwastan Ta Amince Da Tura Kayayyakin Da Aka Kwace Zuwa Sansanin ’Yan Gudun Hijira

Published

on


A ranar Laraba ne hukumar kwastam ta kasa “Nigerian Customs Serbice (NCS)” ta bayar da sanarwa amincewar a kwashe kayayyakin da aka kwace daga hannun ‘yan kasuwa masu fasa kwauri  zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar Borno.

Kayyaykin da suke iya lallacewa wadda jami’an kwastam na “Federal Operations Unit, Zone A” dake Legas suka kwace na da yawa daga cikin kayyakin da za a aika sansanin ‘yan gudun hijiran, kamar yadda Hukumar ta sanar a taron manema labarai data gabatar a Legas.

Shugaban shashen daya gudanar da sintirin kwace kayyakin Mista Mohammed Uba, ya ce, kotu ce ta mallaka wa gwamnatin tarayya kayayyakin bayan da aka shigar da karar kama kayan.

“Ina sanar daku cewa, bayan dukkan ka’idojin kotu da aka bi, kwamitin shugaban kasa akan sansanonin ‘yan gudun hijira wanda shugaban hukumar kwastam Hameed Ibrahim Ali ke shugabanta ya bayar da amincewar a wuce da wadannan kayayakin zuwa ga gwamnatin jihar Borno domin rabawa ga ‘yan gudun hijira, za a yi amfani da sojojin dake kiula da sifir na “Nigerian Army Corps of Supply and Transport (NASCT)” inji Mista Uba.

“Buhunhunan shinkafa masu nauyin Kilogram 50 guda 25,318 (Traila 42) da jarkan mai mai cin Lita 25 guda 3,366 da galan mai guda 175 mai cin Lita 5 da kuma bales guda 1,564 da kuma dilan gwanjo guda 122  da buhu 196 na takalma da kuma takalma guda 938 wanda aka yi amfani dasu. A saboda haka ne kuke ganin manyan motoci sun yi layi a wajen ajiye kayan gwamnati”. Inji shi.

Mista Uba ya kara bayyana cewa, jami’ansa sun kama kayyaki masu yawa da dokar kwastam ta haramta shigo wa dasu, ana kuma sa ran kotu ta mallakawa gwamnatin tarayya kayyakin.

Kayayyakin da aka cafke sun hada da, motocin Toyota Hilud guda 30 ciki har da Toyota Hilud kirar 2018 guda 7 da Toyota Prado jeeps kirar 2017 guda 3 da Range Rober 1 da Ford Edge kirar 2015 guda 1 sauran kayayyakin sun hada da buhunan shinkafa guda 5,516 (Mota Tirela 9 kenan) da naman kaza katan 1,078 da kuma jarkan mai guda 216 da dilan zannuwa guda 173 sai kuma dilan gwanjo guda 683 da kuma tayan mota guda 8 sai buhun taban wiwi mai nauyin Kilogram 134.

Haka kuma an cafke kwantaina 2 masu lamba MSKU130295/2 da MRKU877714/0 da kudaden harajinsu ya kai har Naira Miliyan 25.

 


Advertisement
Click to comment

labarai