Connect with us

WASANNI

Salah Ya Sake Kafa Sabon Tarihi A Liberpool

Published

on


 

Dan wasan Liberpool Mohamed Salah ya sake kafa wani sabon tarihin zura kwallo a gasar firimiyar Ingila, in da kuma ya taimaka wa kugiyar wajen samun gurbi a gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

Salah wanda ya fi zura kwallaye a kakar bana a firimiyar ta Ingila, ya ci wa Liberpool kwallo guda daya a fafatawar da suka doke Brighton da ci 4-0 a ranar  Lahadin data gabata.

Salah ya karbi kyauyar takalmin zinari a matsayinsa na wanda ya fi zura kwallaye a bana a gasar, sannan ita kanta Liberpool ta karrama shi a matsayin gwarzonta na shekara.

A bangare guda ana iya cewa, Liberpool din ta tsallake rijiya da baya, domin kuwa da ta yi sakacin rashin samun nasara akan Brighton, sannan kuma Chelsea ta doke Newcastle, to da babu shakka Liberpool din za ta rikito daga matakin kungiyoyi hudu da ke saman teburin gasar.

A ranar 26 ga wannan watanne Liberpool zata buga wasan karshe na cin kofin zakarun turai da kungiyar Real Madrid a filin wasa na Olympic dake babban birnin kasar Ukraine wato Kieb

A shekarar 1981 dai kungiyoyin sun taba haduwa a irin wannan yanayi na wasan karshe inda Liberpool ce tasamu nasara daci 1-0 ta hannun dan wasa Kennedy.


Advertisement
Click to comment

labarai