Connect with us

WASANNI

Arteta Yana Dab Da Zama Kociyan Arsenal

Published

on


Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa tsohon dan wasan Arsenal kuma mataimakin Guardiola a Manchester City, Pep Guardiola, yana gab da zama sabon mai koyar da kungiyar Arsenal.

Tun bayan da tsohon kociyan kungiyar, Arsene Wenger, ya bayyana cewa zai ajiye aikin koyar da kungiyar aka fara rade radin cewa Arteta, wanda ya shafe shekaru biyar a kungiyar ta Arsenal zai iya maye gurbin na Wenger.

Sai dai banda Arteta akwai masu koyarwar da suka hada da Naggelsmann, mai koyar da yan wasan Hoffenhaim da kuma tsohon dan wasan kungiyar Patrick Biera sai kuma mai koyar da yan wasan Jubentus, Allegri.

Sai dai wani rahoto ya bayyana cewa wanda yafi kowa hannun jari a kungiyar, Iban Gazidiz ya bayyana cewa a shirye yake daya dauki mai koyarwar da bashi da kwarewar koyar da babbar kungiyar indai zai cigaba da koyawa kungiyar irin wanda take bugawa.

A satin daya gabata dai mai koyar da yan wasan Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa bazai hana Arteta komawa Arsenal ba domin fara babban aiki sai dai yace zaifi kowa farin ciki idan yaci gaba da zama da tare dashi a Manchester City.

Rahotanni dai suna cewa duk wanda yazama mai koyar da yan wasan kungiyar shine zai samo wadanda zasu taimaka masa wajen gudanar da ayyukansa na koyarwa da harkokin shugabanci.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai