Connect with us

LABARAI

UTME: Naira Biliyan 1 JAMB Ta Biya Cibiyoyin Rubuta Jarabawa

Published

on


 

Hukumar shirya jarabawar shuga manyan makarantun Kasar nan ta JAMB ta ce, ta biya Naira Biliyan 1 ga masu cibiyoyin (Computer-Based Test (CBT) centres) da hukumar tayi amfani dasu a faDin tarayyar Kasar nan wajen shirya wa Dalibai jarabawar shiga makarantun gaba da firamari a wannan shekarar ta 2018

Jami’in watsa labaran hukumar Mista Fabian Benjamin, ne ya sanar da manema labarai a wani taro da aka gudanar ranar Lahadi a garin Legas, ya ce, biyan kuDin na daga cikin sharuDDan da aka yi da masu cibiyoyin da aka yi amfani dasu wajen gudanar da jarabawar.

Ya Kara da cewa, wannan biya kuDaDen zai tabbatar da danKon zumuncin aiki tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar shirya jarabawar na JAMB da ake yi duk shekara.

“A halin yanzu mun kammala biya Naira Biliyan 1 ga dukkan masu cibiyoiyin CBT da aka yi amfani dasu wajen shirya jarabawar UTME na wannan shekarar 2018.

“Masu cibiyoyin CBT Din sun yi kyakyawan aiki muna kuma yaba da KoKarin da suka yi saboda haka ne muma muke saka musu tabhanyan biyan kuDaDaen da muka shirya dasu cikin lokaci.

“Sai dai mun lura da cewa, akwai wasu cibiyoyin da basu taka rawar day a kamata ba, sun fuskanci matsaloli masu yawa dangane da na’urorinsu, inji shi.

Ya Kara da cewa, Daliban da aka shirya zasu gudanar da jarabawarsu a irin waDanna cibiyoyin dole a ka canza musu wasu wuraren, wanda a halin yanzu waDannan wuraren ne za a biya kuDaDen aikin da suka yi musu.

Mista Benjamin ya ce, al’amarin biyan kuDaDan nada matuKar mahimmanci saboda haka ne zai taimaka a tabatar da ana samun ingantattcen aiki da haDin kai tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar shirya jarabawan.

Daga nan ya Kara bayyana cewar, ba za a biya duk wata cibiya da bata samu daman gudanar da jarabawar ba saboda matsalolin data fuskanta na na’urori, hakan ya zama dole ne domin hukuma ba zata biya mutane da basu yi mata aiki ba, zata biya ainihin waDanda suka yi mata aiki ne. Bayan nazarin hotuna daga na’uran CCTB na wasu cibiyoyin mun lura da inda masu wasu cibiyoyin ke haDa kai da Dalibai masu jarabawa wajen yin maguDi.

“Hukumar bata biya ire iren waDannan cibiyoyi ba kuma a halin yanzu hukumar na KoKarin warware matsalolin da wasu Dalibai suka fuskanta wajen Daukan hoton yatsunsu a lokacin zana jarabawar, za a saurari Korafen daya zama ba wasu dalilai bane daga Dalibai suka jawo da kansu saboda sakaci.

“Baya ga matsalolin Daukan hoton yatsun hannaye, a kwai wasu wuraren da wasu Dalibai suka samu kansu a cibiyoyin da aka gudana da maguDin jarabawa.

“A irin wannan halin ba zai zama anyi adalci ba in a ka soke jarabawan dukkan Daliban dake a cibiyar, saboda haka zamu zaKulo Daliban da babu ruwansu domin basu daman sake zana jarabawar a nan gaba.

“A matsayinmu na hukuma masu mutunci, zamu ci gaba da bai wa Dalibai dama daya kamata na ci gaba da karatu a manyan karantun Kasar nan” inji Mista Benjamin.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai