Connect with us

LABARAI

Rundunar Sojin Sama Ta Aika Da Dakaru 150 Zuwa Jihar Taraba

Published

on


 

Rundunar Sojin sama ta Nijeriya, NAF, ta aike da wata runduna ta musamman da ta Kunshi dakaru 150 ranar Lahadi zuwa sabon matsugunin da ta kafa na bayar da agajin gaggawa a garin Nguruje, da ke Karamar Hukumar Sardauna, ta Jihar Taraba.

Ya zuwa yanzun, rundunar Sojin ta Sama ta kafa shigen waDannan rundunonin na bayar da agajin gaggawa a sassan tsakiyar Arewacin Kasarnan a garin Doma ta Jihar Nasarawa da kuma Agatu ta Jihar Benuwe.

Babban Kwamandan rundunar Sojin saman, SadiKue Abubakar, wanda ya yi wa dakarun jawabi a Jalingo kafin su tashi, ya umurce su da su nu na Kwarewa wajen gabatar da aikin na su.

SadiKue Abubakar, wanda daraktan ayyuka na rundunar, Mista Abubakar, ya wakilce shi, ya ce, ina amfani da wannan daman wajen umurtan ku da ku nu na Kwarewa wajen gudanar da aikin ku.

“Tilas ne a kowane lokaci ku zamanto masu bin dokokin aiki na rundunar Sojin sama da kuma dokokin warware rikici na rundunar Soji ta Kasa.

“Sannan kuma ya wajaba ku kyautata alaKa da mutanan wajen, domin su ne za su taimaka maku wajen gudanar da aikin na ku.”

SadiKue Abubakar, ya ce, waDannan rundunoni na musamman da aka kafa wani sashe ne na tsare-tsaren kafa runduna mai Karfi da za su iya bayar da agaji a kan lokaci duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ya ce, tunkarar matsalolin tsaro a Kasar nan da bukatar wanzar da zaman lafiya ta yadda tattalin arzikin mu zai Karu, su ne suka wajabta kafa wannan sabuwar rundunar ta Nguroje.

Abubakar wanda shi ma bays Mashal ne, ya umurci Sojin da su haDa kai da sauran sassan jami’an tsaro da za su taras a yankin wajen samar da tsaro a Jihar ta Taraba.

Kwamandan na Sojin saman Kasarnan, ya yaba ma Shugaba Buhari, gwamnatin Jihar Taraba da duk waDanda suka taimaka wajen kafuwar sabuwar rundunar.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai