Connect with us

LABARAI

Nan Ba Da Jimawa Ba Za A Warware Rigingimun Jam’iyyar APC, Inji Osinbajo

Published

on


 

 

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayar da tabbacin cewa duk masu ruwa da tsaki kan rigingimun da ke gudana yanzun a Jam’iyyar APC mai mulkin Kasa, kwanan nan za a warware su.

Osinbajo ya bayar da wannan tabbacin ne sa’ilin da yake magana da manema labarai bayan rantsar da Shugaba Julius Bio na Kasar Sierra Leone, a Freetown ranar Asabar.

Fassarar tattaunawar na shi wacce aka raba wa manema labarai ranar Asabar ta hannun babban mai taimaka ma shi kan harkokin manema labarai, Mista Laolu Akande.

Mataimakin Shugaban Kasan ya ce, babu wani sabon abu kan sabanin da ke tsakanin ‘ya’yan Jam’iyyar.

Ya ce, “Kamar yadda ku ka sani ne, siyasa ta gaji Daukan zafi, amma Jam’iyyar namu tana da Karfi, sannan kuma ‘ya’yan Jam’iyyar na mu su na son ci gaba da Dorewar Jam’iyyar da Karfin ta.

“Ina jin mafiya yawan waDannan sabanin duk za a warware su in tafiya ta yi tafiya. Ai haka abin yake, za ka yi ta samun sabani kullum, a kullum za ka ga wasu su ga yadda suke son lamurra su tafi, ina jin ba wata babbar matsala ce ba.”

Osinbajo ya miKa taya murnar Shugaba Buhari ga al’ummar na Kasan Sierra Leone Din, ya kuma yi alKwarin samar da dangantaka mai Karfi a tsakanin Kasashen biyu.


Advertisement
Click to comment

labarai