Connect with us

LABARAI

Kungiyar Masu Jinya Na Asibitin Bauchi Ta Yi Watsi Da Umurnin JOHESU

Published

on


 

‘Ya’yan Kungiyoyin sashin kiwon lafiya na asibitin jihar Bauchi sun yi buris da zancen tafiya yajin aikin sai baba ta gani, suna masu bayyana cewar babu wani umurni da ta zo musu daga uwar Kungiyar gamayyar Kungiyoyin kiwon lafita ta JOHESU illa dai jita-jitan da suke ji wai ana yajin aiki.

Wannan yin burin Din na zuwa ne bayan da uwar gamayyar Kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya ta Kasa wato JOHESU, ta bayar da umurnin kowace Kungiyar da ke KarKashinta su tsunduma yajin aikin sai mama ta gani a bisa wasu haKKoKinsu da suke buKata a wajen gwamnatin tarayya.

Sai dai kuma, reshen Kungiyar ta asibitin jihar Bauchi wato Specialist Hospital har zuwa yanzu suna nan suna ci gaba da aikinsu ba tare da amsa kiran uwar Kungiyar ta Kasa na shiga yajin aikin ba.

A wata hira da ya yi da manema labaru a ranar 11/5/2018 shugaban haDakar Kungiyar jinya da Unguwar Zoma na asibitin Specialist da ke Bauchi, Alhaji Auwal Bello ya bayyana cewar basu da masaniyar kan cewar shugaban Kungiyar JOHESU ya bayar da umurnin tafiya wannan yajin aikin.

Alhaji Bello ya ci gaba da bayyana cewar basu samu wata wasiKa daga haDakar Kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya ta Kasa ba, don haka ne suka ci gaba da gudanar da harKoKin aikinsu kamar yadda doka ta shimfiDa musu “Kasan ana ta magana ana ta ce an-ce-an-ce, ba za ka yi magana da abun da ka ji ana ta cewa ba, sai ka ganshi a rubuce a gabanka,” A cewar shi.

A cewarsa reshen Kungiyar ta asibitin sashin kiwon lafiya da kuma na Unguwar Zoma a shirye suke su shiga yajin aikin da zarar suka samu takarda daga uwar Kungiyar haDakan Kungiyar JOHESU “In suka rubutu mana, a shirye muke mu tafi yajin aikin nan, amma ba za mu taba tafiya ba matuKar ba mu ga umurni daga uwar Kungiya ba. Ba za mu yi amfani da abun da muke ji a gari ba kawai,”

Wasu ‘yan uwan majinyatan da suke kwance a asibitin, sun nuna matuKar farin cikinsu a bisa yin biris da Kungiyar ta yin a batun tafiya yajin aikin, sun nuna fargabarsu kan tafiyar ma’aikatan jinya da Unguwar Zoma cikin yajin aikin domin lafiyar ‘yan uwansu.

Ita dai uwar Kungiyar gamayyar Kungiyoyin jinya (JOHESU) ta tafi yajin aikin ne a makon jiya a sakamakon gazawar da gwamnatin tarayya ta yi na cika musu alKawuran da suka yi a tsakaninsu a lokutan baya.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai