Connect with us

LABARAI

Ku TarwatsaBarayin Shanun Nan Da Mako Uku

Published

on


 

Babban Hafsan rundunar sojojin Nijeriya Janar Tukur Yusuf Buratai ya umurci sojojin dake aikin samar da zaman lafiya a yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna dasu gaggauta share ‘yan ta’addan dake kashe-kashe a yankin a cikin makwanni uku.

‘Yan ta’adda dake harkokinsu a yankin sun kashe fiye da mutane 100 ciki har da sojoji 11 a cikin wata 5.

An ruwaito cewar, sakamakon aiyukan ta’addanci da garkuwa da jama’a a yankin, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kafa barikin sojoji a yankin.

A yayin da yake jawabi a bukin Kaddamar da shirin fatattakar ‘yan ta’addan da aka raDawa suna ‘Operation Idon Raini’ a wajen da ake sa ran kafa barikin sojojin a Kauyen Kanfanin Doka na yankin Birnin-Gwari, Janar Buratai ya ce, yana fatan samun sakamako mai daDi cikin gaggawa da kuma kawo Karshen aiyukan ta’addancin da ake gudanarwa a yankin gaba Daya.

Shugaban rundunar sojojin Nijeriyan ya kuma Kara da cewa, “Daga yanzu ba zamu tsaya sai an kawo mana hari ba, mune zamu kai musu harin, tun da sun kawo mana hari to dole mu kai musu hari tare da murKushesu gaba Daya a duk inda suke.

“Dole a kawo Karshen kashe-kashen da a keyi, dole a kawo Karshen barnata dukiyoyin jama’a ba wai a jihar Kaduna kaDai ba amma a dukkan faDin Nijeriya baki Daya.

“A cikin makwanni 2 zuwa 3 dole a samu sakamako mai kyau da zai durKusar da waDannan ‘yan ta’addan tare da share su gaba Daya.

“Ba daga sama ko wani duniya daban suke zuwa ba, suna nan a cikin yankin, ban san dalilin da ba zaku shiga inda suke ku zaKulosu ba.

“Ina matuKar farin ciki da KoKarin kwamandan ruduna ta 1 da sauran kwamandoji a bisa wannan sabon tsarin, ina nan ina sauraron sakamakon mai kyan a Karshen wannan shirin farmaki da zaku fara.

“Kwamandoji sun riga sun sanar dani irin marsaloli da Kalubalen da kuke fuskanta kuma tuni har mun fara aiki a kan hanyoyin magance waDannan matsalolin.

“Dole mu mayar da martanin daya kamata, dole kuma kwamandoji su Dauki nauyin duk wani matsala da aka samu, saboda haka dole su Dauki mataki a lokacin daya dace, duk kuma wani abu bayan wannan to dole su Dauki alhakin abin daya biyo baya.

“Nan take ya kamata a fara aiki, sauran abin daya shafi kayan aikin da kuke buKata da haKKoKinku zamu yi KoKarin ganin mun samar muku da abin daya kamata” inji Buratai.

Da yake jawabi tun da farko a lokacin da shugaban sojojin ya kai masa ziyara a fadarsa, sarkin Birnin-Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, ya nuna farin cikinsa a bisa kawo sojoji, yana mai cewa, kawo sojojin zai kawo Karshen ‘yan ta’adda cikin Dan KanKanin lokaci.

Sarkin ya ci gaba da cewa, “Ba za a iya maganin waDannan mutanen ta hanyar kafa shinge ko tsayawa a kan hanya ba, saboda haka dole jami’an tsaro su kai wa ‘yan ta’adda yaKi har cikin daji, in ba haka ba, zasu ci gaba da DanDana mana tashin hankali.

“A kwai wasu runduna na musamman da suka yi aiki mai kyau a yankin kwanankin baya, muna ira ga shugaban sojoji, muna kuma buKatar a dawo mana dasu, ana iya haDa su da wasu manyan sojoji da sauran sojoji, na tabbatar in har aka yi haka za a gama dasu da gaggawa, saboda lallai nan ba dajin Sambisa bane, kuma tunda gashi shugaban sojojin Nijeriya ya zo da kansa muna da tabbacin lallai wannan lamarin zai zo Karshe da gaggawa” inji sarkin.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai