Connect with us

LABARAI

Kodin: Kamfanin Emzor Zai Taimaka Wajen Magani Da Tsugunar Da ’Yan Kwaya

Published

on


 

Hukumar gudanarwar kamfanin haDa magunguna na Emzor ta bayyana cewar, zata bayar da gudummawa ga gwamnatin tarayyar Nijeriya wajen tsugunar da kuma bayar da magunguna ga waDanda suna samu matsala saboda shaye shaye.

Kamfanin ta nuna farin cikinta a kan shawarar hukumar NAFDAC, na sake buDe kamfanin bayan da aka sanar da kulle ta kwanakin baya.

Da take bayani a taron manema labarai a Legas, shugaban kamfanin Stello Okoli ta ce, lallai sake buDe kamfanin abin a yaba ne kwarai da gaske.

Hukumar NAFDAC ta kulle kamfanin ne bayan cecekucen da wani shuri na BBC tayi inda aka fallasa matsala da barnar da shan maganin tari mai kodin yake jawo wa a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Shirin da gidan radion BBC tayi ya nuna yadda jami’an kanfanonin haDa magungunan da azurta kansu ta hanyar sayar da maganin Emzolyn mai kodin da kamfanin keyi.

Baya ga kamfanin Emzor, shirin ya kuma fallasa hannun da wasu kanfanoni guda 2 ke dashi a badaKalar sayar da magungunnan tari mai kodin, daga nan ne hukumar NAFDAC ta kulle kamfanin, sai dai bayan ‘yan kwanaki hukumar ta NAFDAC ta sake shawara inda ta bayar da sanarwa buDe kamfanin.

Da take Karin bayani, wata babbar Darakta a kamfanin, Misis Uzoma Ezeoke, ta ce, an sake buDe kamfanin ne bayan tayi gyare gyare daya kamata a tsare tsaren kamfanin, kamfaninmu ya kuma yi alkawarin tsugunar da mutanen da suka kamu da cutar shaye shayen maganin tari mai kodin.

“Kamfanin Emzor zai haDa kai da hukumomin daya kamata a watanni da shekaru masu zuwa domin samar da mafita ga wannan masifar data faDo mana” inji ta.

Ta Kara da cewa, “Daga shirin da BBC tayi, zamu iya fahimtar cewar, a kwai hanyoyin da a za a iya taimaka wajen tsugunar da fitar da mutanen da suka faDa wannan masifar, za kuma mu haDa hannu dasu wajen fuskantar matsalar”

Kamfanin na Emzor ya kuma yaba wa gwamnatin Nijeriya da sauran hukumomi musamman na NAFDAC a bisa Daukan mataki na gaggawa da suka yi a kan wannan lamari dake addabar rayuwar ‘yan Nijeriya.

“Muna jinjina ga ma’aikatan lafiya saboda amsa kiran ‘yan Nijeriya ta hanyar Daukan matakin gaggawa na shawo kan lamarin.

“Ziyarar da hukumar NAFDAC ta kawo kamfaninmu ya gamsar dasu akan matakan da muke Dauka na bin dokoki da Ka’idojin yin magungunna daidai da Ka’idojin da hukumomin ciki da wajen Kasa suka tanada”

“Wannan aminci da muka samu ya faru ne sakamakon aiki tuKuru da amfani da Ka’idoji da hanyoyin sarafa magungunna da ake amfani dasu a faDin duniya, abubuwan da suka faru a ‘yab makwannin nan sun Kara Karfafa mu a kan aiyukan da muke yi, za kuma mu ci gaba da aiki ba gudu ba ja da baya” inji ta.

Ta Kara da cewa, “Kamfanin Emzor ya yi imani da Karfafa matasanmu, ta haka ne muka kafa gidauniyar Chike Okoli a shekarar 2006 domin Karfafa rayuwa mai tsafta da samar da sana’o’i tsakanin matasa, matasa da dama sun amfana da wannan shirin, a halin yanzu wasun sun a gudanar da harkokin sana’o’insu na Miliyoyin Nairori a sassa daban daban na Kasar nan.”

 


Advertisement
Click to comment

labarai