Connect with us

LABARAI

Bayan Shekaru 20 Da Fara Gina Masallacin  Garin Soro, Gwamna M.A Abubakar Ya Taimaka An BuDe Shi

Published

on


 

Dubban  jama’a ne sukayi gangami domin halartar Sallar Juma’ar ta farko a babban masallaci Juma’a na garin Soro wanda aja shafe kusan shekaru ana ginawa bai kammalu ba sai a wannan lokaci da Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ya yi wa masallacin garanbawul aka samu buDe shi.

Mutane suna farin ciki suka cika masallacin ya cika ya batse saboda farin ciki da al’umar garin na Soro da kewaye suke ciki ganin mafarkinsu na yin Sallah a Sabon masallacin ya tabbata a wannan rana Inda suka yi ta sa albarka.

Shi dai wannan masallacin an aza ginshikin gina shi tun lokacin mulkin Gwamna Ahmadu Adamu Muazu amma har ya zuwa lokacin Gwamna M A Abubakar ba a kammala shi ba kamar yadda limamin masallacin ya fada a cikin hudubarsa. Ganin haka ne Gwamna Makama Babba ya bada umarni a sakewa masallacin fasali a kuma kammala aikin masallacin gaba Daya ba tare da bata lokaci ba kuma ya biya kuDi aka yi aikin.

A cikin huDubarsa limamin masallacin  ya mika godiya ta musamman ga Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar bisa wannan aiki na sadaKadatul jariya da ya gudanar a wannan yanki. Ya kuma jagoranci gabatar da addu’o’i na musamman ga Gwamnan da mukarrabansa da suka taimaka wajen ganin wannan aiki ya tabbata.

Wasu daga cikin mutanen garin da suka yi tsokaci da godiya bisa wannan aikin alkhairi na Gwamnan sun ce su a baya har sun fitar da ran za a kammala wannan masallaci suna raye ganin yadda aikin yaKi ci yaKi cinyewa shekara da shekaru amma sai gashi Gwamnan ya gabatar da wannan aiki da ya gagari a baya. Sun roki Allah Ya sakawa Gwamnan Ya biya masa bukatunsa, sun kuma yi alkawarin cewa sufa sai inda Karfinsu ya Kare akan hidimar wannan gwamnati da kuma nema masa goyon baya a lungu da sako a duk lokacin da zabe ya zo.

Shima mai tallafawa gwamna kan ayyukan infanta rayuwar dalibai wajen ciyarwa da shirin n-power Alhaji Mansur Manu Soro ya godewa gwamnan jihar Bauchi kan wannan aiki kuma ya buKaci jamaa su ci gaba da yi masa adduah don ya samu iko da zarafin ci gaba da taimaka wa mutane kan dukkan bukatun su.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai