Connect with us

LABARAI

Ana Kan Gyaran Hanyoyi 300 –Fashola

Published

on


 

 

A yanzun haka akwai kimanin hanyoyi 300 da ake kan aikin gyaran su a duk sassan Kasarnan, Ministan Ayyuka, Gidaje da Lantarki ne Babatunde Raji Fashola, ya bayyana hakan.

Da yake magana jiya wajen buDe taro na 4 na wakilan direbobin tanka, a Abuja, Fashola, cewa ya yi, wannan gwamnatin ta Dauki lamarin gina hanyoyi da gyara waDanda ake da su da mahimmanci domin bunKasa tattalin arzikin Kasa.

Cikin jawabin na shi mai taken, ‘Roads in Nigeria and the Impact of Petroleum Products Distribution’, cewa ya yi, akwai hanyoyin da gwamnati ta fi mayar da hankali a gyaran na su da ta yi wa laKabi da, A1-A4, sune hanyoyin, Legas-Shagamu- Benin-Ore -Sakkwato;  Warri-Benin-Okene-Lokoja-Kano; Fatakwal-Enugu-Onisha-Yobe; Kalabar-Makurdi-Maiduguri.

Ya ce hanyoyin masu daraja ta biyu a wajen gyaran na su sune waDanda suka haDa kayan noma da kasuwanni da garuruwa a duk faDin Kasarnan.

Sauran sune waDanda suka sada tashoshin Jiragen ruwa da cibiyoyin ilimi.

Gwamnati kuma ta fara aikin gyaran wasu gadoji na musamman kamar gadar Tamburawa da, gadar Third Mainland bridge da gadar Tatabu.

Fashola ya ce, gwamnatin da ta gabata a kasafin kuDin ta na shekarar 2015, bilyan 18 kacal ta kebe wa gyaran hanyoyin Kasarnan sannan kuma Naira bilyan tara ne kaDai ma suka biya, amma ya zuwa yanzun wannan gwamnatin ta kashe sama da Naira bilyan 250 a kan manyan hanyoyi.

Fashola ya ce, ba wata Jiha a Kasarnan da ba ta sami aikin hanyan ba na wannan gwamnatin, ya Kara da cewa, tuni ‘yan kwangila sun koma bakin ayyukan su na aikin manyan hanyoyin a dukkanin sassan Kasarnan.

Fashola ya gargaDi dirobobi da su guji yin mugun gudu, ya ce, rashin hanyoyi masu kyau sune sanadiyyar kashi 10 kacal na haDurran da ake yi a hanyoyin alhalin mugun gudu shi ke da alhakin sama da kashi 75 na haDurran da ke aukuwa bisa hanyoyin.

Ministan ya yi nu ni da cewa, baya ga mugun gudun, sauran dalilan da ke haddasa haDurran sun haDa da sabawa dokokin hanya, rashin lafiya da kuma shan muggan Kwayoyi.

A jawabin sa, Shugaban na Kungiyar ta NUPENG, Kwamared Williams Akporeha, cewa ya yi, duk da cewa wannan gwamnatin tana yin aiki tuKuru wajen inganta manyan hanyoyin namu, amma dai akwai bukatar Kara mayar da hankali kan hakan sosai.

Ya ce, “Kan haka, muna kira ga gwamnatin tarayya da ta shelanta dokar ta baci kan aikin hanyoyin Kasarnan domin ta Kara mayar da hankali sosai. Domin ba wani tattalin arzikin da zai samu ci gaba ba tare da hanyoyi a Kasa masu lafiya ba.”

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai