Connect with us

LABARAI

A Bauchi: An Sauya Wa Kwalejin COE Kangere Suna Zuwa Adamu Tafawa Balewa

Published

on


 

Gwamnan jihar Bauchi Lauya Muhammad Abdullahi Abubakar ya amince da sauyin sunan Kwalejin Ilimi ta Kangere (COE Kangere) zuwa sunan Kwalejin Ilimi ta Adamu Tafawa Balewa, Kangere.

Bayanin hakan na Kunshe ne a cikin wata kwafin sanarwar manema labaru wacce jami’in watsa labarai na kwalejin Ilimi ta Kengere, Bala Baban Kawu ya sanya wa hanu haDe da raba wa manema labaru a jiya a Bauchi.

Takardar wacce mai riKon muKamin magatakardar kwalejin Hajiya Hadiza Usman, ta shaida cewar amincewa da sauya sunan da gwamnan Bauchi ya yi, na zuwa ne biyo bayan da majalisar dokokin jihar ta amince da hakan, kana kuma majalisar zastarwa na jihar ita ma ta amince da hakan domin tunawa da irin gudunmawar da wanda aka sanya sunansa ya bayar wajen ci gaban jihar ta Bauchi.

Magatakardar, ta kuma yi kira ga ma’aikatu, sashi-sashi, bangarorin gwamnati, bangarori masu zaman kansu da sauransu da su sanya lura haDe da yin amfani da wannan sauyin da aka yi cikin gaggawa.

LEADERSHIP A Yau ta rawaito cewar kwalejin an samar da ita ne tun a shekara ta 1984 domin samar da kwalejin yaKi da jahilci wacce take KoKarin koyar da manyan mutanen waDanda basu samu zarafin yin karatu a lokacin da suke samartaka ba, hakan kuma na cikin manufar yaKi da jahilci haDe da samar da wadattaccen ilimi ga jama’an jihar ne, inda aka sauya kwalejin daga makarantar yaKi da jahilci zuwa kwalejin ilimi ta Kengere a shekara ta 2015.

Har-ila-yau, sanarwar manema labarum ta kuma bayyana cewar, kwalejin ta jinjina da KoKarin gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar a bisa maida hankulansa wajen tabbatar da ci gaban kwalejin a kowani lokaci.

Yanzu haka dai sunan Kwalejin Ilimi wacce ta ke KenKeshe Malamai da ke Kangere ana kiranta da suna Kwalejin Ilimi ta Adamu Tafawa Balewa ne.

A kwanakin baya ne dai, majalisar zastarwa na jihar Bauchi ta bayyana cewar sanya sunan Adamu Tafawa Balewa wa kwalejin, na zuwa ne biyo bayan irin gagarumar gudunmawar da ya taka wajen gina jihar Bauchi haDe da samar da jihar zuwa matakin da take a yau, don haka ne  gwamnatin jihar, majalisar dokokin jihar da majalisar zastarwa na jihar suka amince da hakan domin tunawa da gudunmawarsa ga jihar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai