Connect with us

LABARAI

2019: Buhari Ya Cancanci Sake Neman Shugabancin Nijeriya –Ngige

Published

on


 

Ministan Kwadago, Mista Chris Ngige, ya bayyana cewa, shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai sake lashe zaben da za a gudanar a shekarar 2019 saboda cancanta da karbuwar a faDin tarayyar Kasar nan.

Miata Ngige ya bayyana haka ne a yayin da yake tattaunawa da sabbin shugabannin jam’iyyar APC na Karamar hukumar Idemili South ta jihar Amanbara ranar Lahadi data gabata.

Ministan ya ce, lallai shugaba Buhari ya yi rawar gani kuma ya cancanci a sake zabansa a matsayin shugaban Kasar Niieriya.

“Ina tsayuwa a gabanku a yau tare da sanar daku cewar, shugaba Buhari ya yi aiki daidai gwargwado a kowanne fanni na rayuwar Kasar nan.

“Buhari zai samu gaggarumar nasara a zaben za a gudanar na shugabancin Kasar nan a shekarar 2019” inji shi.

Mista Ngige, ya kuma tabbatar da cewar, jam’iyyar APC zata yi takarar dukkan muKaman da za a yi takararsu a zaben da yake tafe, yana mai cewar, jam’iyyar zasu samu nasarar samun Kuri’u fiye da kashi 70 na Kuri’un da za a kaDa a jihar Amambara.

Ya kuma yaba wa ‘yan jam’iyyar a bisa KoKarinsu na tabbatar da samun nasarar zaben shugabanin jam’iyyar na Kananan hukumomin 21 na jihar a ranar Asabar data gabata.

Ma’ajin jam’iyyar APC na jihar Mista George Moghalu, ya jinjina wa ‘yan jam’iyyar a bisa nasarar da aka samu na zaben shugabannin jam’iyar a faDin jihar.

“Ina mai Kwarin gwiwar cewar, za a samu irin wannan nasarar a zaben shugabannin jam’iyyar na jihar dake tafe nan gaba” inji Mista Moghalu.

Sauran masu ruwa da tsaki a taron sun yi alkawarin aiki tare don ganin jam’iyyar ta samu gaggarumar nasara a zaben shekarar 2019.

 


Advertisement
Click to comment

labarai