Connect with us

LABARAI

Mun Kusa Kammala Shirin Fara Hako Danyen Man Fetur A Bauchi –Maikanti Baru

Published

on


 

Shugaban ma’aikatar danyen man fetur da albarkatun kasa ta Nijeriya (NNPC) Dakta Maikanti Kachalla Baru ya bayyana cewar shirye-shiryen fara hako danyen man fetur a kauyen Kolmani da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi ya kusa kammaluwa domin fara hako dan fetur din.

Maikanti wanda ya bayyana hakan a cikin wata makala da ya gabatar a ranar Juma’ar nan da ta gabata a sa’ilin da ke jawabi na musamman a cikin bukukuwan yayen daliban jami’ar ATBU da ke Bauchi su dubu 8,495 da ya gudana a ranakun Juma’a da Asabar a cikin jami’ar da ke Bauchi.

Ya ce, “A kan kogin Kolmani muna cin gaba da aikin fara hako danyen man da ke wannan yankin wanda nan gaba kadan za mu kai ga farawa,” in ji shi, yana mai cewa hukumar ta NNPC ta yi dukkanin shirye-shiryen da suka dace wajen ganin an samu nasarar fara hako man a wannan kauyen, inda yake bayanin cewar kawo yanzu, dukkanin alamu suna yi musu nuni da cewar za a iya samun mai din a wannan kogin da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi.

Baru ya kuma kara da cewa, “Za mu fara aikin hako danyen albarkatu da ke kogin Kolmani, sannan za kuma mu kafa rijiyoyin hako mai din gabanin karewar wannan shekarar,” In ji Baru.

Baru Kachalla ya bayyana cewar daga cikin nasarorin da gwamnatin Buhari ta iya cimmawa a sashin albarkatun mai sun hada da ci gaba da aikin hako man fetur da ke tafkin Gongola wanda ya hada Bauchi da Gombe.

Kan wadannan ci gaba da aiyukan binciken man fetur din, Baru ya bayyana cewar suna nan suna ci gaba da aikin hada ne a tsakanin jami’ar ATBU, Bauchi da kuma jami’ar Modibbo Adama Unibersity of Technology, Yola domin samun nasarar gudanar da dukkanin bincike na kwararrun da ake da bukata kan wannan aikin nemo man da suke malale a yankunan.

Shugaban ma’ikatan mai ta kasa, Baru ya bayyana cewar NNPC tana daukan nauyin karatun wasu daliban tun daga matakin kasa har zuwa sama domin samun nasarar habaka sashin binciken mai da kuma samar da ilimi mai nagarta a kasar nan.

Tun da fari ma, ya gudanar da Laccarsa ne a kan gudunmawar hada hanu a tsakanin jami’o’i da kuma masana’antu domin ci gaban kasa Maikanti ya hakikance kan cewar kasashe da daman gaske sun samu ci gaba ta fuskacin hada karfi da karfe a tsakanin masa’antu da kuma jami’in kasarsu, don haka ne ya yi kira ga jami’’o’in kasar nan das u fara koyi da hakan domin samar da ci gaba.

Ya bakin shugaban albarkatun danyen man fetur ta kasa, “Wasu kasashen sun ci gaba sosai, sun samu ci gaban nan ne ta hanyar hada kai da masa’antu da kuma jami’o’i wajen fitar da kasa za ta ci gaba. Don haka ne muke kira ga sauran jami’o’i da suke koyi ko kuma su samu wasu wadanda suka yi aiki da ma’aikatu su kawosu su domin su zama ma’aikatansu domin a samu kaiwa ga nasarar da ake nema. Samar da alaka mai ma’ana a tsakanin jami’o’i da kuma masana’antu ci gaban da za a samu a kasar nan zai taimaka gaya,” In ji shi.

MaiKanti ya bayyana cewar idan aka samu kulla kyakkyawar alakar a tsakanin jami’o’I da masa’antu, za a samu gagarumar ci gaba musamman ta fuskacin habaka tattalin arzikin kasa domin wasu abubuwan da za su cikin sauki, yana mai bayar da misalai da wasu kashen da suka yi zarra, har ma ya kawo misali da wasu ababen da ya dace a maida hankula wajen yin hadaka a kansu.

Wannan taron yayen daliban dai shi ne karo na 23, 24 da kuma karo na 25 wanda aka hada aka gudanar waje guda, inda aka yaye dalibai su dubu 8,496 kamar yadda mukaddashin shugaban jami’ar ta ATBU Farfesa Saminu Abdulraman Ibrahim ya shaida a wajen yaye, yana mai bayanin cewar sun samu gagarumar nasarori tun bayan hawansu wannan kujerar, inda kuma ya sha alwashin daurawa daga inda aka tsaya.

Da yake jawabi a wajen yaye, Saminu ya baya sosai wa tsohon muddashin shugaban jami’ar a bisa tasa gudunmawarsa, sai ya yi alkawarin daurawa daga inda aka bashi kujerar domin ci gaban jami’ar, jihar Bauchi da kasar Nijeriya baki daya.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai