Connect with us

LABARAI

Jihohi Sun Raba Naira Biliyan 593 Daga Asusun Tarayya

Published

on


 

Jihohi 36 na tarayyar kasar nan zuwa yanzu sun karbi Naira Biliyan 593.1 daga asusun tarayya a matsayin kudaden shiga a zango na farko na wannan shekarar 2018.

Bayanin haka ya fito ne a rahoton wata wata da hukumar asusun rarraba kudaden kasa “Federation Account Allocation Committee (FAAC)” ta fitar, kamar yadda kanfanin dillancin labarai na NAN ta samu a Abuja ranar Lahadi.

Hukumomin gwamnatin da suka zuba kudade a cikin asusun sun dada da kanfanin mai na kasa na  “Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC)” da hukumar tattara kudaden shiga na kasa “Federal Inland Rebenue Serbice” da hukumar Kwastam.

A watan Janairu, jihohi 36 sun rarraba Naira Biliyan 196.99 a tsakaninsu. A watan Fairairu kuma sun raba Naira  Biliyan 195.25 yayin da suka raba Naira Biliyan 200.86 a watan Maris na wannan shekarar (2018).

An raba kason ne ta hanyar amfani da tsarin rabon tattalin arzkin kasa inda ake bai wa gwamnatin tarayya kashi 52.68 jihohi kuma su dauki kashi 26.72 yayin da kananan hukumomi ke daukar kashi 20.60 cikin abin da aka tattara.

Rahoton ya nuna cewar, sai da aka cire basussukan da ake bin bangarorin gwamnatin kafin a raba kudaden. Abubuwan da ake bin jihohi a zangon farko sun hada basussukan cikin gida dana kasashen waje da kudaden ‘yan kwangila da sauransu.

Wasu kudaden da aka cire wa jihohin sun hada dana shirin farfado da aiyukan samar da ruwa dana aikin bayar da tallafin kimiyya ga aikin gona na tarayya da kudaden samar da takin zamani da shirin samar da ruwa na jihohi da shirin aikin gona na jihohi da kuma na shirin aiyukan fadama na kasa.

Rahoton ya nuna cewa, bayan an cire kudaden da ake binsu bashi a wannan zangon farko na shekarar 2018 kowanne jiha a cikin jihohi 36 na kasar nan ya karbi kudade kamar haka;

Jihar Abia ta karbi Naira Biliyan 13.09, Adamawa Naira Biliyan 11.82, Akwa Ibom Naira Biliyan 50.88, Anambra Naira Biliyan 13.01, Bauchi Naira Biliyan 13.04, Bayelsa Naira Biliyan 38.89, Benue Naira Biliyan 12.98, Borno Naira Biliyan 14.82 yayin da jihar Cross Riber ta karbi naira Biliyan N8.41.

Rahoto ya nuna cewar, jihar Delta ta samu Naira Biliyan 49.43, Ebonyi  Naira Biliyan 10.73, Edo Naira 15.86 Biliyan, Ekiti Naira 8.75, Enugu Naira N12.27, Gombe Naira 10.17, Imo Naira Biliyan 12.72, Jigawa Naira Biliyan 14.2, Kaduna Naira Biliyan 16.15 jihar Kano kuma ta samu Naira Biliyan 19.65.

Haka kuma kason jihar Katsina daga asusun tarayya na wata ukun farkon wannan shekarar ya nuna cewa ta karbi Naira Biliyan13.99, Kebbi ta karbi Naira Biliyan 12.78, Kogi Naira Biliyan 12.39, Kwara Naira Biliyan 10.62, Legas Naira Biliyan 29.99, Nassarawa Naira Biliyan 11.18 jihar Neja kuma ta samu Naira Biliyan 13.44.

Daga karshe rahoton ya nuna cewa, jihar Ogun ta karbi Naira Biliyan 9.4, Ondo Naira Biliyan 15.27, Osun Naira Biliyan 4.98 billion, Oyo Naira Biliyan 13.83, Plateau Naira 10.15, Ribas Naira Biliyan 42.74, Sokoto Naira Biliyan 12.43, Taraba Naira Biliyan 11.1, Yobe Naira Biliyan 12.42 yayin da jihar Zamfara ta karbi Naira Biliyan 9.16.

Kanfanin dillancin labaran NAN ya tabatar da cewa, hukumar FAAC ta kunshi kwamishinonin kudi da Akanta Janar na jihohi 36 na tarayyar kasar nan. Ministan kudi na tarayya Nijeriya ke zama shugaban kwamitin yayin da Akanta janar na tarayya da wakili daga hukumar NNPC ke zama wakilai a kwamitin.

Sauran mambobin sun hada da wakilai daga hukumar tattara kudaden shiga na kasa “Federal Inland Rebenue Serbice” da hukumar Kwastam da babban bankin kasa CBN.

Dokar data kafa asusun tarayya ta samar da raba kudaden da aka tara tsa

 kanin fallen gwamnati guda uku, gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi da kuma kananan hukumomi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai