Connect with us

LABARAI

Ibeto Ta Yi Sabon Hakimin Ibelu

Published

on


 

aga Muhammad Awwal Umar, Minna

An zabi Malam Muhammadu Muktar Husaini Ibeto a matsayin sabon Ibelun Ibeto da ke karamar hukumar Magama ta jihar Neja.  An zabi sabon Ibelun ne bayan rasuwar mahaifin shi Alhaji Husaini Ibelu ranar takwas ga watan hudu na shekarar da muke ciki, sabon hakimin Ibelun dan kimanin shekara talatin da uku da haihuwa, an yi zaben ne jiya laraba a fadar Ibelu da ke garin Ibeto.

Da yake zantawa da wakilin mu, sabon hakimin Ibelun ya nuna farin  cikin shi akan zaben shi da aka yi a matsayin Ibelun Ibeto, kuma yayi kira ga wadanda suka yi neman  sarautar tare da su zama masu hakuri da tawakali, kuma su zo a hada hannu domin ciyar da masarautar gaba, cigaban masarautar ita ce abin alfahari gare mu.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, mataimakin shugaban karamar hukumar Magama Hon Sani Doma Ibeto, ya nuna farinciki bisa ga yadda aka fara neman  wannan sarautar lafiya, aka kuma kammala lafiya. Sai dai yana jawo hankalin  wadanda suka yi takarar kujerar da su hada kai da sabon Ibelun domin ganin masarautar ta cigaba, domin masarautar ta zama abin alfahari ga al’ummar masarautar. A kallan har wanda ya samu nasarar dare kujerar ta Ibelu su goma sha biyu suka yi takara wadanda sun hada har Iyayen sabon Ibelun.

Ana bangaren kuwa, mahaifiyar sabon Ibelun, Hajiya Balkisu Ibelu ta yi kira ga sabon Ibelun da cewar yasan fa ba shi kadai ya nemi wannan kujerar ba, kuma ba yafi sauran ba ne, domin a cikinsu ba kaninsa kusan duk Iyaye ne sai yannai a gare shi, saboda haka ya budw ido da kyau domin ya ba su girmansu a matsayinsu na iyayen shi su kuma su girmama shi a matsayi Hakimin  ibelu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai