Connect with us

LABARAI

Bayanan Kashe-kashen Da Majalisar Dattawa Ta Fitar Abin Takaici Ne -’Yan Sanda

Published

on


 

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta yi tir da sakin bayanan zarge-zargen kashe-kashen da Majalisar Dattijai ta yi, ta na mai cewa, hakan zai iya kara tabarbara matsalar tsaro ne a kasar nan.

Rundunar ta ce, tana kan hanyar magance matsalar kashe-kashen da ke aukuwa a wasu sassan kasarnan, ta kara da cewa, tuni har ta gurfanar da mutanan da ta kama bisa zargin aikata hakan.

“Sakin wadannan bayanan kashe-kashen da aka yi a shekarar 2018 da ofishin Shugaban Majalisar Dattaijai ya yi abin mamaki ne, bai kuma kamata ba, zai kuma iya kara tabarbara matsalan tsaro ne a kasarnan.

“Abin takaici ne da tsoro a rika yin siyasa da rayukan mutane. Bayanan kuma zato ne kawai da ba wata shaida a kansu. Ofishin na Shugaban Majalisar ta Dattawa, bai bi hanyar samun wadannan bayanan ba daga wani ofishin rundunar ta ‘yan sanda,” in ji Rundunar cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Asabar ta hannun Kakakin ta, Jimoh Moshood.

Rundunar ta yi ikirarin cewa ta gano sama da haramtattun makamai 5000, a hannun mutanan da ba su dace ba a sassan kasarnan, ta ce ta sanya mataimakin Shugaban ‘yan sanda da ya je ya yi wa Majalisar bayanin matakan da take dauka domin magance matsalar tsaro a kasarnan, amma sai majalisar ba ta bari ya yi mata bayanin ba.

Rundunar ta musanta bayanin da Kakakin Majalisar, Sanata Sani Abdullahi, ya yi na cewa, ba sun gayyaci Shugaban ‘yan sanda ne kan kamun da suka yi wa, Sanata Dino Melaye ba, bisa zargin sa da safarar makamai.

Rundunar ta bayyana mamakin ta kan tugun da Majalisar ta shirya wa Shugaban ‘yan sandan na nannagan sa a talabijin bainal jama’a, ta ce ai ba zai yiwu a tattauna matsalar tsaro irin wannan a cikin mutane ba.

Rundunar ta ce, tun hawan Shugaban ‘yan sandan ya bayyana a gaban Majalisar har sau 10 kan abubuwa daban-daban masu mahimmanci da suka shafi kasa, ta ce Idris ya na matukar girmama Majalisar.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai