Connect with us

LABARAI

Ban Zagi Fashola Da Amaechi A Littafina Ba –Ngozi Iweala

Published

on


 

Tsohuwar ministan kudi Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, ta kwankwashi wadanda ta kira magumata dake kokarin aran bakin ta su ci mata albasa, inda suke cewan wai ta ce tsaffin gwamnonin nan Rotimi Amaechi da Raji Fashola, wadanda a haklin yanzu ministoci ne ‘yan maula ne.

Dakta Okonjo-Iweala, wadda it ace ministan kudi a zamanin gwamnacin tsohon shugabann kasa Olusegun Obasanjo, tana mayar da martani ne a kan labaran dake yawo a kafafen watsa labarai inda aka ce wai ta ce, tsaffin gwamnonin ‘yan maula ne a jiya a yau kuma sun zama ‘ya  lelen gwamnati mai ci.

Ministar kudin, wanda ta rike mukamin har sau biyu, an ce tayi wannan bayanin ne a cikin littafinta mai take “Yaki da rashawa nada hatsari” ‘Fighting Corruption is Dangerous’.

Dakta Okonjo-Iweala, wadda ta kuma rike mukamin kula da tsarin tattalin arzikin kasa a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta ce, kalaman da ake yada wa ba nata bane. Okonjo-Iweala ta ce, “Babu wani wuri a cikin littafin nawa mai suna ‘Fighting Corruption is Dangerous’, dana ce ‘yan maulan jiya sun zama ‘yan lelen yau”

“Duk da cewa, ina matukar godiya da irin tattaunawa da muhawarar da littafin ya janyo a ciki da wajen kasar nan, masu gulmace-gulmace da zagon kasa ya kamata su nemi littafin su karanta domin su bayar da gudunmawa a ilimance maimakon su rika yawo da surutan da bashi da amfani”

A rahoton da yake yawo a kafafen yada labarai, an ce wai Okonjo-Iweala tayi bayani ne a kan irin matsalolin data fuskanta a kokarinta na tabbatar da gwamnatin Nijeriya tayi abin daya kamata a lokacin da aka samu garabasar karuwar kudaden man fetur.

Ga rahoton da ake zargin ta ce.

“Rotimi Amaechi a matayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya ya kalubalanci gwamnatin tsohon shugaba Jonathan a lokacin da ya yi kokarin adana kudaden da aka samu na rarar man fetur, har da ma Fashola da mafi yawan gwamnonin jam’iyyar APC, yanzu sune kuma ke ihun cewar, jam’iyyar PDP bata adana komai ba, munafukai makaryata kawai”

“A lokacin mun fito da shirin da zai tallafa wa tattalin arzikin ta hanyar bude asusun banki na rarra man fetur, kudin da muka tara har ya kai Dala Biliyan 22.

“A shekarar 2008, a lokacin da kudin man fetur ya fadi warwas daga Dala 148 zuwa Dala 38 a kan kowanne gangan mai, babu wanda ya ji labain matsala a Nijeriya domin daga cikin wadannan kudade ne kasa tayi ta amfani, ina kuma matukar alfahari da wanna nasarar.

“A lokacin dana sake dawowa a shekarar 2011, kudin dake a cikin asusun ya dawo Dala Biliyan 4 kacal, saboda an yi amfani da wasu daga cikin kudaden wajen fuskantar shirin yafewa ‘yan taratson Neja Delta da gwamnatin Umaru Musa ‘Yaradua ya fito dashi, duk da cewar kudin gangan mai ya yi matukar tashi a lokacin.

“Na sake kokarin adana kuda a lokacin, shugaban kasa ya yarda amma gwamnoni suka ki yara da wannan shirin.

“Na fuskanci matsaloli da yawa daga wajen su, abin ya kai da har sai da aka yi shari’a har zuwa kotun koli. Sai gashi yanzu da kasa ke bukatar wadannan kudade suna zargi ma da rashin adana kudaden.

“In da Nijeriya tayi kata tsantsan dab a a haka muke ba, abin na damu na. muna da dukan kwarewar da ake bukata amma a ka hana mu yin abin daya dace.

“Abin takacin shi ne ‘yan maulan da suka sha room jiya sai gashi wai yau sun zama ‘yan lelen da basa laifi a yau.”

Okonjo-Iweala, wadda kuma babbar jami’a ce a kanfanin Lazard Ltd, Board Chair Gabi da kuma hukumar AfricanRiskCapacity, ta ce, rahoton da ake yawo dashi aiki ne na ‘yan barada masu neman bata mata suna a idon duniya.

Daga karshe ta sake shawartar duk wanda yake bukatar bayar da gudummawarsa a kan littafin daya nemi littafi ya karata ya kuma bayar da gudumawa mai ma’ana.


Advertisement
Click to comment

labarai