Connect with us

LABARAI

An Shirya Taron Bita Ga Malamai Masu Tafsiri A Jihar Neja

Published

on


 

An nemi malaman da zasu gabatar da tafsirin wata Ramalan na wannan shekarar da su mayar da hankali wajen hada kan al’umma da zaman lafiya. Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi kiran a lokacin bude taron yini biyu ga malaman tafsiri kan muhimmancin anfani da hikimar Alkur’ani mai girma wajen hada kan al’umma da zaman lafiya da ya gudana a dakin taro na gidan matasa da ke Bosso Estate.

Gwamnan da ya samu wakilcin dan majalisar dokokin jiha, mai wakiltar karamar hukumar Rafi, Hon. Danlami Bako. Ya ce makasudin shirya wannan taro a karkashin hukumar kula da harkokin addinai, shi ne samar da kafa ta hadin kan al’umma ta yadda za a samu ingantaccen zaman lafiya a jiha.

Da yake karin haske bayan gabatar da kasidarsa, babban limamin Nupe, Sheikh Adamu Yakatu, wanda ya samu wakilcin Alhaji Yusuf Alfa Yakatu, ya bayyana ladar falalar azumin ramalan da anfanin zaman lafiya a cikin al’umma, wanda wajibi ne malamai su cire bambance-bambancen da ke tsakanin wajen karantar da mutane addini.

Ya ce ramalan wata mai tattare da alherai duk wanda ya aikata wani abu na alheri za rubanya masa lada, dan haka jawo hankalin malamai da su yi anfani da kwanukan ramalan wajen nusar da al’umma alherai.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, wakilin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Neja, babban limamin masallacin rundunar ‘yan sanda, DSP Yakubu Tahir, ya jawo hankalin malamai muhimmancin zaman lafiya, ya ce rundunar su za ta baza jami’an tsaro cikin kaki da farin kaya dan sauraro masu irin abubuwan da zasu rika wakana a wajajen tafsirai, babban burin rundunar ‘yan sanda bada tsaro da kula zaman lafiyar al’umma.

Dakta Bashir ‘Yankuzo, daya daga cikin malaman da suka halarci taro ya yabawa hukumar da ma gwamnatin jiha kan yadda suka hada fuskokin malamai masu akidu daban- daban kuma aka amince akan a tafi akan akida daya wato Alkur’ani da Hadisi, wannan na nuna irin tasirin fahimtar da ke tsakanin su, hakan kuma wannan dama ce na gane cewar kiyayya a tsakanin malamai ba alfanu ba ne, ina jawo hankalin malamai da su rike abubuwan da aka zaburar da mu akai dan anfani da shi wajen gina tubalin zaman lafiya a cikin al’umma.

Da yake karin haske ga manema labarai, babban darakta a hukumar kula da harkokin addinai, Dakta Umar Faruk Abdallah, ya ce manufar shirya wannan taron ga malaman addini musulunci su ne suyi anfani da lokuttan ramalan wajen kyautata alakar jama’a, hadin kai da zaman lafiya.

Ya ce gwamnatin jiha tana bukatar duk da samuwar akidun da ba su sabawa addini da dokokin kasa ba, akwai bukatar samar da yana yin da zai hada kan mabiya, su fahimci cewar akidun ba su ne asali ba illa hanya ce ta neman kusanci da koyi kamar yadda Manzon ya yi.

Taron dai ya samu halartar kungiyoyin Darika, IZALA da kungiyoyin yarbawa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai