Connect with us

LABARAI

An Bukaci Malamai Da Su Gabatar Da Wa’azin Hadin Kai A Cikin Watan Ramadan

Published

on


 

Ganin yadda al’ummar musulman kasar nan a na duniya baki daya ke shirin shiga watan Azumin Ramadan mai albarka, ya sa mutane suka fara kiraye kirayen cewar, yakamata malamai masu gabatar da wa’azi su mayar da hankali wajen anfani da watan domin hada kan al’ummar musulmi, musamman a lokacin da za su gudanar da tafsirin alkur’ani a masallatai ko a wuraren taruwar jama’a.

Kira na baya bayan nan ya fito ne daga bakin Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo, a lokacin da yake zanatawa da manema labarai kwanakin a kan shire shiryen shiga wata mai alfarma. Mumuda Liman ya ce, a halin yanzu babu abin da musulmi suka fi bukata irin hadin kai da taimakon juna

Ya ci gaba da bayar da misalin yadda wadanda ba musulmai ba a kasar nan da sauran kasashen duniya kullum kansu a hade yake, tare kuma da taimakawa juna ta fannoni da dama.

Wani abu kuma da malaman za su kara mayar da hankali wajen fadakar da al’umma a watan na Ramadan shi ne addu’oin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali domin duk kasar da babu zaman lafiya ba za ta samu ci gaban da ake bukataba. “Kar amanta Allah na amsar addu’oi tare da shafe zunubai duk dai acikin watan na Ramadan”. Inji shi.

Malam Mamuda Liman yayi amfani da wannan dama da kira ga ‘yan kasuwar jihar Kano, da na kasar nan cewa, su yi wa Allah da Annabi su guji karin farashin kayayyaki a cikin watan mai albarka, musamman kayayyakin da aka fi bukata a lokacin gudanar da azumin na Ramadan.

Ya ce, abin kunya ne ace sai a watan ne wasu ‘yan kasuwar ke kara farashin kayayyaki mai makon ace a samu rangwame a cikin watan. Ya ce, masu hali suma na da rawar da za su taka sosai wajen tallafawa marasa galihu musamman ta hanyar ciyarwa da kuma bayar da kyaututtuka ga al’umma da kuma tallafawa marayu.

Gwamnatocin da suke ciyarwa  a cikin watan suma yana da kyau su kara rubanya kokarinsu ganin yadda ake cikin halin matsin rayuwa. Sai ya yi addu’ar Allah ya sa a fara azumin lafiya a gama lafiya, Allah ya amshi ibadun da al’ummar musulmai za su gudanar a cikin watan na Ramadan.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai