Connect with us

LABARAI

Ya Kamata  Apc Ta Magance Barakar Da Ke Kunnowa Game Da Zaben Shugabanni  –  Tijjani Gamawa

Published

on


An shawarci shugabannin jam’iyyar APC da masu rike da mukamai a Nijeriya da su hamzarta dinke barakar da ke kunnowa a tsakanin magoya bayan jam’iyyar tun daga lokacin da aka fara yunkurin gudanar da zabukan jam’iyya cikin makon da ya gabata amma yawancin mutane ke nuna rashin gamsuwa game da yadda lamurra ke gudana har zuwa wannan lokacin.

Air comodo Ahmed Tijjani Baba Gamawa mai ritaya babban mai ba kakakin majalisar tarayya shawara, shine ya yi wannan kira cikin hirarsa da manema labarai a Bauchi inda ya kara da cewa tun farko yana  son jan hankalin  ‘yan siyasa  su kasance suna gudanar da ayyuka bisa bin doka da tsari da bin dokokin jam’iyya don a samu ci gaba kan abin da suka sa a gaba na inganta siyasa saboda  a tafi tare a gudu tare a tsira tare.  Amma idan mutane kalilan suka bi son zuciya to lamarin ba zai haifar da da mai ido ba a fagen siyasar APC saboda mutane a halin yanzu idon su a bude ya ke game da lamurran siyasa.

Don haka  Ahmed Tijjani Baba ya bayyana cewa aikata ayyukan son zuciya da karya doka da neman gina wasu mutane kalilan ba abin da za su haifar sai nadama a fagen siyasa don haka ya kamata a yi hattara kan abin da mutane suke so da wanda basa so don a samu ci gaban jam’iyyar APC. Ya ce yin karan tsaye ko kama karya bai dace da wannan jam’iyya ba wacce ta kafu a kan gaskiya da adalci. Amma idan aka wayi gari wasu mutane kalilan suka ce za su ci gaba da murde mutane wajen yin abin da suka ga dama hakan zai iya haifar da matsala a fagen siyasar wannan lokaci saboda kowa ya san abin da ya dace don ciyar da jam’iyya da kasa gaba.

Tijjani Baba Gamawa ya bayyana cewa abubuwan da ke faruwa a Jihar Bauchi game da siyasa fada ne na cikin gida kuma suna so shugabannin jam’iyya da masu rike da mukamai su hada kan magoya baya don a zauna a daidaita a dinke baraka a tafi tare ba tare da samun matsala ba, matukar ana son a ciyar da wannan jam’iyyar gaba ya kamata a lura da matsalar da ke kunnowa a gyara don a tafi tare a tsira tare.

Hakan shine zai taimaka jam’iyyar ta ci gaba da rike tagomashin ta na siyasa har ta fiskanci zabuka masu zuwa a yi su cikin nasara.

Game da ziyarar da shugaban kasa Buhari ya kai Amurka a kwanakin baya, Ahmed Tijjabi Baba Gamawa ya bayyana cewa wannan ziyara ce mai kyau da za ta taimaki Nijeriya wajen inganta tsaro da tattalin arziki musamman wajen magance matsalar rigingimu da suke aukuwa da yake yake da ake yi sun tattauna kan matsaloli da dama kuma akwai zaton ziyarar za ta haifar da ci gaban tattalin arziki da wanzuwar zaman lafiya a Nijeriya.

Don haka ya bukaci ‘yan Nijeriya su ci gaba da yin addu’ah tare da ba gwamnati goyon baya don a samu ci gaba da gina kasa yadda ya kamata.


Advertisement
Click to comment

labarai