Connect with us

LABARAI

Na Kai Kara Kotu Game Da Yadda Zabukan APC Su ka Gudana A Bauchi –Sanin Malam

Published

on


Dan takarar shugabancin jam’iyyar APC a Jihar Bauchi Alhaji Sani Shehu Sanin Malam ya bayyana rashin gamsuwa game da yadda aka fara gudanar da zaben gundumomi na jam’iyyar APC a Jihar Bauchi cikin makon da ya gabata, inda ya bayyana cewa tuni ya garzaya kotun Abuja don ganin an sake tsarin yadda aka gudanar da zaben ta hanyar rusawa a sake sabo wanda mutane za su gamsu.

Alhaji Sani Shehu Sanin Malam ya  bayyana wa wakilin ta wayar tarho daga Abuja cewa ya kai kara gaban babbar kotun tarayya a Abuja don kalubalantar yadda aka ce an  gudanar da zaben alhali ba wanda ya ga masu zabe ko alamun takardar cikewa, duk da kasancewar an sa sun tura kudi mai yawa banki da nufin sayen form don shiga takarar neman shugabancin jam’iyya amma ana so a yi wasa da hankalin su a mayar da su kamar basu san ‘yancin su na siyasa ba, alhali duk masu shirya wannan almundahana cikin siyasa suka same su kuma da su aka kafa APP har ta koma APC ba su taba zuwa ko ina ba duk wata nasara da aka samu da taimakon su aka same ta har zuwan wannan gwamnati ta Buhari tun da ya fara shiga takara suke tare.

Alhaji Sanin Malam ya kara da cewa tuni an samu baraka cikin jam’iyyar APC kuma ba za su hakura kan abin da ya faru ba, suna son a sake shugabancin jam’iyyar a duk inda ake da muradin zabe kowa ya shigo a fafata wanda ya samu nasara shike nan wanda kuma bai samu ba haka Allah ya yi. Inda ya bayyana cewa a kowa ce Jiha akwai wannan korafi don suna da yawa wadanda suka samu tirjiya daga masu son zuciya kuma ba gudu ba ja da baya sai sun bi hakkokin su a kotu an yi abin da ya dace da doka don a zauna lafiya a ci gaba da gina jam’iyya.

Ya kara da cewa mutane da yawa suka  sayi tela a banki don shiga takarar madafu dabam dabam na kujerun shugabancin APC tun daga gunduma zuwa Jiha amma duk an yi watsi da su an mance abin day a faru a baya ga jam’iyyar PDP wacce ta yi nufin kama karya mutane suka taru suka bijire suka dawo APC da wasu jam’iyyu aka karya ta don haka ya kamata ayi hattara kar mutane su fusta su kai makura lamarin ba zai yi dadi bag a duk wani mai son ci gaban dimokuradiyya a Nijeriya.

Sanin malam ya kara da cewa kuma suna nufin sun yi asarar kudi da suka sayi form  kenan duk da cewa akwai akwai dokokin jam’iyya da dokokin tsarin mulkin kasa na yadda aka shirya gudanar da zabukan siyasa? Don haka ya bayyana cewa abin da aka yi ya zamo wajibi a waiwaici lamarin kuma a hukunta wadanda suka shirya duk wani magudi amma yana nan daram wajen neman shugabancin jam’iyyar APC shi ne yasa ya ajiye mukamin sa na mai ba gwamnan Jihar Bauchi shawara kan ayyuka na musamman don shiga takarar shugabancin jam’iyyar APC a jihar Bauchi amma wasu mutane kalilan ke son yin wasa da hankalin su da fatar uwar jam’iyya za ta yi taka tsantsan don a ci gaba da gina jam’iyya tad ore da martabobin ta.


Advertisement
Click to comment

labarai