Connect with us

LABARAI

Baby Gafa Ta Jinjinawa Dakarun Sojin Najeriya Kan Samar Da Zaman Lafiya

Published

on


Hajiya Habiba Garba da ake kira Baby Gafa, ta jinjinawa jami’an tsaron Sojin Najeriya na yadda suke ta kokarin shawo kan lamuran tsaro da ya addabi shiyar arewa maso gabashin Najeriya dama wasu yankunan kasar.

Hajiya Baby Gafa, ta jinjinawa jami’an tsaron ne a lokacin da take zantawa da LEADERSHIP A YAU LAHADI, inda tace samun shugabani na gari masu kishin kasa da al’ummar su ne yasa aka samu zaman lafiya ya dawo a wanann shiya ta mu da ma kasar mu.

Ta ce da ba dan jami’an tsaron mu masu kishi bane da har yanzu Najeriya na cikin wani hali na rudani saboda ba wanda yasan halin da yake ciki saboda tabarbarewar tsaro musamman a arewa maso gabas da rikicin Boko haram ya daidaita.

Baby Gafa, yar siyasa ce kuma tsohuwar shugabar Mata ce ta jami’ar ANPP a lokacin tsohuwar gwamnatin Alhaji Abubakar Habu Hashidu Matawallen Dukku, kuma ta bada gudumawa sosai wajen ci gaban harkokin Mata a jihar Gombe wacce har yanzu ake damawa da ita a siyasar jihar.

A cewar ta ko anan jihar Gombe gwamnatin jihar karkashin jagorancin mai girma Talban Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, shi ma ya bada gudumawa wajen shawo kan lamuran tsaro a jihar domin ya taimakawa jami’an tsaro yadda ya kamata su kuma suka sami damar gudanar da aikin su wanda yanzu kowa a jihar Gombe yana barci idon sa a rufe.

Hajiya Baby ta kuma ce uwa uba shugaban kasa Muhammadu Buhari, shi ne ya tsaya tsayin daka ya zagulo hazikan jami’an tsaro masu kishin al’umma da Najeriya ya damka musu amana suka hana idon su barci suke kare rayuka da dukiyoyin al’umma har aka cimma wannan mataki.

Kamar masu fade-faden cewa a canja dakarun jami’an tsaron Najeriya ta ce to ta ina suka gaza idan kuma aka canjasu su wadanne iri za’a kawo za su samu lokaci na taka rawar da wadanda aka canja din za su yi kafin su daidaita komai an mayar da hannun agogo baya dan haka maganar canja su ba ta taso ba a yanzu.

Ta kara da cewa idan akwai ta inda suka kasa ne to shawari za’a bayar a kara musu kayan aiki sannan kuma a ci gaba da taya su da addu’a dan ganin sun kara samun kwarin guiwa wajen shiga lungo da sako suna kawar da miyagun nan.

A wani gefe kuma ganin an kusa shiga watan azumi wata mai dimbin albarka ta yi kira ga shugabanin masallatai da cewa kar a sake a dinga shiga masallatai haka kawai ko wuraren tafsirai a sa ido sosai wajen aiki da masana tsaro dan gudun kar a sake wasu su shiga da miyagun abubuwa su kashe mutane.

Daga nan sai Baby Gafa ta bai wa jama’a hakuri da cewa duk wanda za a caje shi a lokacin da yazo shiga masallaci ko wurin wa’azi kar ransa ya baci domin rashin sanya idon ne yake haifar da halaka rayukan al’umma masu yawa amma idan aka sa ido ko za’a samu barna za ta zo da sauki.

 


Advertisement
Click to comment

labarai