Connect with us

LABARAI

Azumin Ramadan: Yobe Ta Ware Miliyan 65.5 Domin Masu Karamin Karfi

Published

on


A shirye-shiryen tunkarar azumin watan Ramadan, na wannan shekarar, gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya amince da ware naira miliyan 65.5 domin shirya abincin buda-baki ga  masu karamin, a kwanakin azumin watan Ramadan, a wasu cibiyoyi na musamman a duk fadin jihar Yobe.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin babban jami’in hulda da kafafen yada labarai a ofishin gwamanan jihar Yobe, Malam Abdullahi Bego, ya bayyana cewa za a kashe wadannan kudin ne wajen shirya abincin buda-baki ga masu azumin tare da sauran ayyukan da suka jibanci azumin irin su gudanar da wa’azi da tafseer, wanda ma’aikatar harkokin addinai a jihar zata sa ido wajen gudanar dasu.

Bugu da kari kuma, bayanin ya fayyace cewa za a yi amfani da naira miliyan 48.5; daga cikin adadin, wajen sayen raguna da kayan alatu wadanda za a raba a cikin wadannan cibiyoyin buda-baki 42 a fadin jihar, yayin da kuma za a kashe naira miliyan 15 wajen baiwa malamai masu wa’azi, dan abin hassafi a lokacin azumin.

“Maigirma Gwamna, Alhaji Ibrahim Gaidam ya amince da a ware naira miliyan 63.5 ta hanyar ma’aikatar harkokin addinai wajen shirya abincin buda-baki ga masu karamin karfi a cibiyoyi 42 da aka tsara dake kananan hukumomin 17, a fadin jihar Yobe kuma hadi da abin hasafi ga malaman da zasu gudanar da tafseer a watan azumin”. Inji sanrwar.

“Kuma daga cikin wadannan kudin, za a yi amfani da naira miliyan 48.5 wajen sayen raguna da za a yanka da sauran kayan alatu na girki, da za a raba a cibiyoyi 42, inda kuma aka ayyana kashe naira miliyan 15 wajen baiwa malamai masu wa’azi da tafseerin al-Kur’ani Mai Tsarki alawus-alawus, a cikin watan azumin.”

Malam Abdullahi Bego ya sake nanata cewa “Bugu da kari kuma, Maigirma Gwamna ya amince da a ware shinkafa buhu 1, 260 tare da jarkokin man girki 630, domin ciyarwar a wadannan cibiyoyi 42 da aka tsara, a cikin wannan wata na Ramadan”.

Duk da yadda shekaru da dama gwamnatin jihar Yobe ta sha ware irin wadannan makudan kudi, wajen shirya abincin buda-baki domin taimaka wa masu karamin karfi, amma kuma kowacce shekara abin yana kasancewa kamar rijiya ta bayar guga ta hana, duba ga yadda jama’ar da ake yi domin su ke korafin basu gani a kasa ba. Saura da me, ko bana kwalliya zata biya kudin sabulu? Wanda lokaci ne kawai zai iya bayar da wannan amsar.

Yayin da wasu ke bayar da shawarar cewa, yana da kyau gwamnatin jihar Yobe ta rinka nada kwamiti a karkashin amintattun mutane kuma masu dattaku, domin samun nasarar ciyarwar tare da tabbacin an baiwa wadannan malamai masu gudanar da wa’azi da tafseer alawus din da aka tsara basu. Sun ce, amma da sauran rina a kaba, matukar ba a yiwa wannan tufakar hanci ba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai