Connect with us

LABARAI

Akwai Hatsari A Haramta Mallakar Makamai, Cewar Basaraken Abuja

Published

on


Wani basarake a Babban Birnin Tarayya Abuja, Sarkin Shanu, Alhaji Shehu Musa Aljan, ya bayyana cewa, akwai hatsari da fargaba mai yawa kan yadda babban sufeton ’yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya haramta wa al’umma wadanda ba jami’an tsaro ba, mallakar makamai, ya na mai cewa, miyagun mutanen da su ka ki mika nasu makaman za su iya yin amfani da wannan dama su rika aikata manyan laifuka, kamar fashi da makami, garkuwa dsa mutane, kisan gilla da azabtarwa, cikin sauki, saboda sun san cewa, yanzu duk mutanen kirki ba za su iya kare kansu ba.

Don haka Shehu Aljan, wanda kuma shi ne mai bai wa kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) shawara kan harkokin tsaro, ya soki lamirin rundunar ’yan sanda ta kasa kan daukar wannan mataki na amshe makamai daga hannun jama’ar gari ba tare da ta nemi cikakkiyar shawara ba.

A tattaunawarsa da manema labarai a Abuja cikin makon nan, Alhaji Aljan ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya sake duba wannan mataki da babban sufeton ya dauka ta hanyar kyale masu lasisi da su cigaba da makaman, in ya so a dauki tsattsauran mataki kan wadanda ke amfani da makamai ta hanyar cutar da wasu ko duk wata hanya wacce ba ta kamata ba.

Ya kuma yi zargin cewa, “akwai masu garkuwa da mutane da dama, ’yan fashi da makiyaya mahara a babban birnin tarayya wadanda ’yan kungiyar sa-kai ta banga su ka kama su ka mika wa ’yan sanda, amma daga bisani sai a ka sake su bisa zargin bayar da cin hanci ga jami’an tsaron.”

 


Advertisement
Click to comment

labarai