Connect with us

LABARAI

Yau Ake Jana’izar Khalifa Isyaka Rabi’u A Kano

Published

on


A yau Juma’a ne ake jana’izar shugaban Darikar Tijjaniyya na Nijeriya, Sheikh Isyaka Rabi’u wanda ya riga mu gidan gaskiya ranar Talatar da ta gabata a birni Landan na kasar Birtaniya.

Gwamnatin Jihar Kano ta ba da hutu ga ma’aikata domin samun damar halartar jana’izar.

Milyoyin al’ummar Musulmi daga sassan kasar nan da waje ake sa ran su hakarci jana’izar.

Tarihi daibya nuna cewa a Unguwar Jingau cikin birnin Kano aka haife shi a 1928 ba a garin Tinki ba, gidansu yana nan a lungun da yake kallon gidansu Gali Umar Na’abba.

Kakanninsa kuma hijirarsu daga Kukawa kusan shekaru dari uku ne, kaburburansu suna nan a kauyukan Tinki da Saye a cikin karamar hukumar Bichi.

Daga kansa har zuwa mutum goma sha biyu daga cikin kakanninsa duka mahaddatan Alkur’ani mai girma ne.

Ana kyautata zaton yi masa sallar jana’iza ranar juma’a mai zuwa a masallacin Sheikh Muhammadu Rabi’u bayan sallar juma’a.

Allah ya jaddada masa rahma, amin.


Advertisement
Click to comment

labarai