Connect with us

LABARAI

Matasa 4,905 Ke Neman Aikin Kurtun Dansanda A Jigawa

Published

on


Kimanin matasa 4,905 ne wadanda suka fito daga kananan hukumomi 27 da ke fadin Jihar Jigawa ke fafutukar neman aikin kurtun Dansanda wadda ake kan yi a yanzu.

Mataimakin sufeto janar na kasa mai kula da bangaren walwala da samar da kayayyaki, DIG Maigari Abbati Dikko ne ya bayyana haka jiya a lokacin da yake duba yadda ake aikin tantance matasan a hedkwatar ‘yansandan da ke birnin Dutse.

Ya ce, babu ko shakka a wannan karon, gwamnati ta dauki tsauraran matakai domin tabbatar da cewa, an dauki matasan da suka cancanta gami da toshe duk wata kafa da ake zargin za ta kawo ba da cinhanci a yayin tantancewar.

Ya ce, a yayin tantancewar wannan karon, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a dauki sabbin ‘yansandan kimanin 6,000 a kasa baki daya.

Haka kuma ya ce, a yayin daukar sabbin ‘yansandan za a tabbatar da cewa kowacce karamar hukuma da ke fadin kasar nan ta samu rabonta.

Sannan ya kara da cewa, jarrabawar za a gudanar da ita ta hanyar hukumar JAMB domin rage magudi yadda kowa zai sami sakamakonsa nan take cikin mintuna.

Daga karshe ya yi kira ga matasan da su fallasa duk wani mutum da ya nemi cinhanci a hannunsu a yayin tantancewar neman aikin.


Advertisement
Click to comment

labarai