Connect with us

LABARAI

Kujerar Gwamna: ‘Yan Majalisar Nasarawa Sun Amince Da Takarar Silas Agara

Published

on


Kakakin Majalisar dokokin Jihar Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi ya bayyana cewa ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun amince da takarar Silas Agara matsayin Gwamnan jihar a zaben 2019.

Ya bayyana haka a A ranar Talata lokacin da dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa karkashin inuwar tutar Jam’iyyar APC wato mukaddashin Gwamna Al-makura Hon.Silas Ali Agara ya kai ziyara ga yan Majalisar dokokin Jihar a zauren Majalisar dake kan titin Shanda cikin garin Lafia.

‘Yan majalisa goma sha tarane cikin Ishirin da hudu karkashin jagorancin Kakakin Majalisar dokokin Jihar Nasarawa Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi suka tarbi dan takarar Gwamnan Hon.Silas Ali Agara yayin ziyarar tashi.

Bayan bude taro da adu’a sarkin yakin niman zaben Hon.Silas Agara.

Alhaji Yusuf Loko ya kaddamar da tawagar da suka rufawa dan takarar baya daya bayan daya . sanan ya bayyana makasudin zuwanasu ya kuma yi godiya ga ‘yan Majalisar da suka amsa tayinsu suka basu irin wanan lokaci mai mahimmanci domin ganawa da dan takarar Gwamnan a zauren Majalisa.

Daga nan  Kakakin Majalisar ya bukaci yan Majalisar kowa ya gabatar da kansa da mazabersa.bayan gabatar da kansune .

Hon.Silas Ali Agara ya bayyana makasudin zuwansa zauren Majalisar da cewa ya ziyarci ya’yan Jam’iyyarsa ta APC ne saboda ya jaddada masu aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa domin ya gaji mai gidansa Gwamna Umar TANKO Al-makura a zaben 2019 mai zuwa .

Hon. Agara yace kamar yadda alumman Jihar Nasarawa suka bukaci dayafito takarar Gwamnan saboda ganin cancantarsa .yace wanan abin ya kara masa kwarin giwa nayin takarar Gwamnan a Jihar Nasarawa saboda samun goyon bayan alumma.

Silas Ali Agara yayi fatan samun hadinkan yan Majalisar da goyon baya domin ciyar da Jihar gaba. yakara da cewa su auna sugani idan ya cancanta kamar yadda alumman Jihar suke cewa to yana niman goyon bayansu su taimaka su hada kai domin cigaban Jihar dama Jam’iyyar APC baki daya .

Shima da yake jawabi a madadin yan Majalisan dokokin Kakakin Majalisar Jihar Nasarawa Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi ya jinjinawa mukaddashin Gwamna dangane da yadda yake gudanar da ayyukansa na cigaba da kuma yadda yake biyaya ga tafiyar Gwamna Al-makura yadda tafiyarsu tayi dai dai kowa ke yabawa da salon mulkinsu .

Kakakin Majalisar yace ;abin ayabane idan aka samu Gwamna da mataimakinsa sun aiki tare kansu a hade komai zakatarar yana cigaba.

Kakakin Majalisar Hon.Ibrahim Balarabe Abdullahi ya nuna farincikinsa da yadda Mukaddashin Gwamna ya fito takarar niman kujerar Gwamnan a shekarar da yadace.

Yace ; Mukaddashin Gwamna mutumne kwarere Wanda ya dace da wanan kujerar saboda gogewarsa da yadda aka dade ana damawa dashi a cikin Gwamnatin Jihar.

Kakakin Majalisar yace muna mika goyon bayanmu ga wanan takarar taka kuma zamu mara maka baya idan lokaci yayi .

Yace ; abin farin cikine Jam’iyyar APC ta marawa jiga jigai irin wadannan wadanda tarihi yasan dasu a siyasan Jihar Nasarawa.

Sanan yayi fatan Allah ya nuna mana zaben 2019 Lafiya Allah yabamu nasara shima Dan takararmu na Gwamna Allah yabashi sa’a.

Silas Ali Agara wanda ya dade ana damawa dashi kuma ya rike mukamai iri dabam dabam .

Mukamin mukaddashin Gwamna ba kowani Dan siyasane zai iya rikewa a kare Lafiya da shiba .Hon.Silas Ali Agara yana kara samun karbuwa wajen alumman Jihar Nasarawa.

Tundaga lokacin da ya kadamar da kansa a ofishin Jam’iyyar APC da sunan mai niman kujerar Gwamnan Jihar.

Alumman keta tururuwa suna sanya kafa a tafiyar Hon.Silas Ali Agara domin .ganin ya zama Gwamnan Jihar Nasarawa a shekarar 2019.

Hakan ya sanya Leadership ayau ta tattauna da wasu jama’a masu gogoriyon ganin Jam’iyyar APC ta tsayar da Mataimakin Gwamnan a kujerar Gwamnatin Jihar a zaben 2019.

Hajiya Hauwa ta kasance tare da Dan takarar a zauren Majalisa take cewa kadubi dubban jama’a da suka biyo Hon. Agara ba komai yake basuba illa iyaka soyayya da suke nuna masa.

Kuma ba komai yasa jama’a ke kaunarsaba sai saboda ganin yadda Mukaddashin yake kyautatawa alumman Jihar a duk lokacin da suke bukatar ganinshi kofarshi a bude yake .

Shima Malam Shuaibu Abdullahi yace: farinjinin Hon. Silas Ali Agara tana shiga zukatan alumman Jihar Nasarawa a kowani lokaci . yace : Hon. Agara mutumne da yasan ya kamata kuma mai hangen nesa .yace: Agara yanada gogewa a harkokin mulki saboda andade an gudanar da Gwamnati tare da shi a wanan Jihar.

Yakara da cewa idan APC taba Hon.Silas Agara kujerar takarar Gwamnan zata samu gagarumin nasara a zaben 2019.

Kuma Agara zai daurane daga inda maigidansa Gwamna Al-makura ya tsaya saboda yasan inda aka tsaya karasawa za’a yi .

Mukaddashin Gwamna Jihar Nasarawa Hon.Silas Ali Agara.

 


Advertisement
Click to comment

labarai