Connect with us

LABARAI

Jerin Sahun Hamshakan Duniya: Dangote Ya Sha Gaban Mataimakin Shugaban Amurka

Published

on


Babban hamshakin dan kasuwan kasarnan, Aliko Dangote, ya shiga jerin manyan mutane 75 mafiya karfi a duk fadin duniyar nan, ya ma yaga wa mataimakin shugaban kasar Amurka, Mike Pence. Cewar Mujallar nan mai bin diddigi ta, Forbes, a bayanin binciken da ta fitar kan mutanan da suka fi kowa karfi da buwaya a duniyar nan, na wannan shekarar ta 2018.

Dangote ya yi kafada da kafada da manyan shugabannin duniyar nan kamar, Di Jinping, shugaban kasar China, Bladimir Putin, shugaban kasar Rasha da, Donald Trump, Shugaban kasar Amurka, wadanda suka zo a lamba na daya, na biyu da na uku bi-da-bi.

Dangote, yana kan lamba ta 66 ne, a matsayin dan adam na 66 da shida mafi buwaya a wannan shekarar a duk duniya, yana kuma saman Mataimakin Shugaban kasar Amurka, Mike Pence, wanda ya zo a lamba ta 67, da kuma Kamar Jabed Bajwa, babban buwayayyen dakaren Shugaban Rundunar Sojin kasar Pakistan, wanda shi kuma ya zo a lamba ta 68.

Attajrin attajiran na Afrika, shi ne kadai dan Nijeriyan da sunan sa ya bayyana cikin jerin hamshakan na duniya, shi ne kuma mutum na biyu dan Afrika a cikin jerin sunayen, gudan dan Afrikan shi ne, Shugaban kasar Misira, Abdel-Fatah el-Sisi, wanda yake kan lamba ta 45 cikin jerin sunayen.

A baya dai Mujallar ta Forbes, ta shelanta cewa, Dangote, shi ne bakin fata guda tilo da yake a cikin jerin sunayen, da ta fitar a shekarar 2016. baya ga Shugaban kasar Amurka na wancan lokacin, Barack Obama, inda a can a ka lissafta shi a lamba na 71 sama da mai neman shugabancin kasar ta Amurka a wancan lokacin, Donald Trump, wanda ya zo a lamba ta 72.

Dangote, shi ne shugaban rukunin kamfanonin Siminti na Dangote, wanda yake samar da metric tan milyan 44 a duk shekara a nahiyar Afrika, a hakan ma tunanin kara fadada kamfanin da kashi 33 yake yi, ya zuwa shekarar 2020.

A cewar Mujallar ta Forbes, kan bayanin jerin masu kudin na duniya, ya zuwa watan Maris na shekarar 2018, Dangote, ya mallaki tsabar kudin da suka kai dala bilyan 14.1, hakan ya kai shi shiga jerin masu kudin duniya 100, kuma wanda ya fi kowa arzikin kudi a nahiyar Afrika kwata, matsayin da ya rika har kusan shekaru goma ba a sami wanda ya zarta shi ba.

Dangote, ya kai matuka ne a shekarar 2014, sa’ilin da ya zama attajirin attajiran duniya na 23, ya kuma yaga wa Shahararren mai kudin nan mai ruwa biyu, Saudiyya-Habasha, Mohammed Hussein Al Amoudi, a shekarar 2013, da sama da dala bilyan 2.6, inda ya zama attajirin attajiran duniya dan asalin nahiyar Afrika.

 


Advertisement
Click to comment

labarai