Connect with us

LABARAI

Hukumar Shige Da Fice Ta Yi Sabon Yunkuri Kan Tsaron Iyaka

Published

on


Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Muhammad Babandede ya umurci manyan shugabannin hukumar na jihohi su 36 har da na Babban Birnin Tarayya Abuja su kara matsa kaimi a kan sintirin tsaron kan iyakoki tare da wayar da kan al’umma game da illar tafiye-tafiye kasashen ketare ba bisa ka’ida ba.

Har ila yau, shugaban ya kara zaburad da jami’an da ke sintirin su zage damtse kan ayyukansu, kana ya umurci jam’an hukumar da ke aiki a mashigi kan-tudu, da ruwa da filayen jiragen sama su tabbatar da cewa daukacin mutanen da ke shigowa kasar nan da wadanda suke fita suna hakan ne tare da ingantattun takardun da suka halasta musu tafiye-tafiyen.

A wani bangare na wayar da kan jama’a game da hadarin safarar mutane zuwa kasashen waje da shigo da ‘yan gudun hijira ta haramtacciyar hanya, hukumar ta nemi al’umma su nemi sanin hadarin da ke tattare da haramtattun tafiye-tafiye kamar yadda yake kunshe a cikin kundin da aka kaddamar mai taken “Fasfo don tafiya salim alim”.

A karkashin wannan sabon yunkurin, za a raba wa masu tafiye-tafiye zuwa waje da ke neman fasfo da wadanda ke tsallakowa zuwa cikin kasar nan kundin kyauta, a wani bangare na gangamin wayar da kan jama’a.

Hukumar Shige da Fice ta Kasa ta wallafa kundin a karkashin Gidauniyar Hadin Gwiwar Kungiyar ECOWAS da Kasar Andulus kan shige da fice.

Hukumar ta yi kira ga al’ummar kasa kowa ya yi kawance da ita wajen wayar da kan jama’a masu tafiye-tafiye game da mugun hadarin da ke tattare da fita ko shiga kasar nan ta haramtacciyar hanya.

Sanarwar da ta fito daga jami’in hulda da jama’a ta hukumar, Mista Sunday James ta yi fatan wannan sabon matakin da aka dauka zai karfafa sintirin tsaron kan-iyaka tare da rage hadarin tafiye-tafiye ta haramtacciyar hanya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai