Connect with us

LABARAI

Dabido Ya Mallaki Jirgin Sama Na Kashin Kansa

Published

on


Shahararren Mawakin nan dan Nijeriya, Dabid Adeleke, wanda aka fi da kira, Dabido, ya sayi jirgin sama samfurin Jet domin amfanin kansa, wanda hakan ya mai she shi matashin farko cikin matasan Nijeriya bakidaya da ya mallaki jirgin sama.

Dabido, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twita mai adireshin, @iam_Dabido, ranar Laraba.

Mawakin ya yi sanarwa a shafin na shi kamar haka, “Na fa rigaya na saya, ba wasa ne ba. gumin kaina ne!”

Dabido, dan shekaru 26, ya yi wannan sayayyan mai dankaren tsada ne, makwanni biyu kacal da ya saya wa Budurwar sa, Chioma Abril, 23,  wata tsaleliyar mota samfurin Porsche, ta isassu mai dan Karen tsada ta Naira milyan 45, inda ya danka mata ita kyauta a matsayin taya ta murnar zagayowar ranar haihuwan ta.

Ya zuwa yanzun dai, Dabido, bai yi karin haske ba kan siffofin jirgin saman na shi da ya saya, da kuma yawan kudin da ya narka wajen sayen na shi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai