Connect with us

LABARAI

Zan Kammala Gina Tituna Kilomita 1,300 A 2019 – Gwamna Badaru

Published

on


Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar ya lashi takobin kammala ayyukan tituna masu tsawon kilomita 1,300 kafin karshen shekarar 2019.

Gwamnan ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya karbi bakoncin Ministan wutar lantarki, Aiyuka da gidaje Baba Tunde Raji Fashola a fadar gwamnatin jihar dake birnin Dutse.

Ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar samarda ingantattun tituna a fadin jihar kasancewar samuwar tituna na daya daga cikin muhimman abubuwa dake bunkasa tattalin arziki ‎da cigaban kasa baki daya.

‎Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatinsa ta gaji ayyukan tituna masu tsawon fiye da kilomita 700 wadanda kaso arba’in kacal tsohuwar gwamnati ta gudanar amma gwamnatinsa ta dora kan wadannan ayyuka.

Gwamnan ya kuma ce, bayan kammala wadannan ayyukan tituna da suka gada zuwa yanzu gwamnatinsa ta kuma bayarda wadansu sabbin ayyukan titunan wadanda tsawonsu ya kai samada kilomita 230 a fadin jihar.

Sannan ya bada tabbacin cewa, cikin wadannan ayyukan tituna da ya gudanar, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zo domin bude wasu daga cikinsu nan bada dadewa ba.

Daga karshe ya yi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da marawa yunkurin gwamnati baya domin ciyar da jihar Jigawa gaba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai