Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

‘Yanjarida Ke Tona Asirin Galibin Badaqalar Cin Hanci A Kasar Sin

Published

on


Ya zama al’ada a kasashen duniya duk inda ake da ‘yanjarida su kafa kungiya domin habaka cigabansu da kuma kare hakkokinsu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
‘Yanjaridan kasar Sin sun yi wa kansu kiyamullaili tun tale-tale inda suka kafa Babbar Qungiyar Xaukacin ‘Yan Jaridan Kasar (All-China Journalists Association) a shekarar 1937 a Birnin Shanghai, babbar cibiyar kasuwancin kasar. Zuwa yanzu kungiyar za ta cika shekara 81 da kafuwa idan Allah ya kai mu watan Yuli mai zuwa.
A ranar 26 ga watan Afirlun da ya gabata, Tawagar wakilan Kamfanin Buga Jaridun LEADERSHIP ta ziyarci shalkwatar kungiyar a Birnin Beijing, babban birnin kasar Sin inda shugabannin kungiyar a karkashin daraktan hulda da kasashen waje na kungiyar, Mista Rong Changhai da wani jami’in sashen, Mista Nicolas Zhang suka tarbi tawagar.
Da yake jawabi ga tawagar, Mista Changhai ya yi bayani game da manyan aikace-aikacen da kungiyar ke aiwatarwa da suka shafi bunkasa cigaban ‘yanjaridan kasar da kuma kare hakkinsu.
A cewarsa, “Kungiyar Daukacin ‘Yanjaridun Kasar Sin ta mayar da hankali sosai wajen horas da editocin kafafen yada labarai daban-daban da sauran ma’aikata game da kwarewa a kan ayyukansu. Horaswar ana shirya ta a kai a kai duk lokacin da aka samu dama. Kungiyar tana kuma sanya ido sosai da karfafa yadda danjarida zai rika ladabtar da kansa a yayin gudanar da aiki ba sai ya jira wani ya nuna masa ba”.
Daraktan ya kara da cewa a wani bangare na kara wa ‘yanjarida kaimin gudanar da ayyukansu, kungiyar takan shirya bikin ba da lambobin yabo ga wadanda suka yi fice a fagen aikinsu, yana mai cewa “muna shirya bikin ba da kyaututtuka da lambobin yabo ga Editoci goma da suka fi nuna kwazo a kan aikinsu. Da wani da muke shiryawa domin ba da lambobin yabo ga ‘yanjaridu goma mafiya kwazo da sauran ire-irensu”.
Da aka tambaye shi game da hanyoyin da suke bi wajen samun kudaden aiwatar da wadannan bukukuwa, Mista Changhai ya ce “muna samun kudin gudanar da wadannan abubuwa ne daga kudin ka’ida da mambobin kungiya ke biya, sannan gwamnati takan dauki nauyin wasu hidindimun, haka nan kungiyoyin fararen hula da ke cikin kasa (Sin) su ma suna tallafawa”.
Ganin cewa cewa duk inda danjarida yake an san shi da taimaka wa cigaban kasa da al’ummarta, ko ta wane bangare ne ‘yanjaridan kasar Sin suke taka rawa ga cigaban kasar?, Daraktan ya yi bayanin cewa “akwai sassa da dama da ‘yanjaridan kasar Sin ke ba da gudunmawa ga cigaban kasa. Suna mayar da hankali wajen ba da rahotanni masu ma’ana ta kowane fanni. Tattalin arziki, zamantakewa, al’ada, cigaban zamani da sauran su. Sannan galibin badakalar cinhanci da rashawa a nan kasar ‘yanjarida ne suka bankado suka tona asirin masu yi. Wannan ya sa ake amfani da wani karin magana a kasar nan cewa “mutum ya yi hankali, ya kula da muhimman abubuwa guda biyu: danjarida da kundin aiki (file)”.
Da shi ma yake karin bayani kan aikace-aikacen kungiyar, Mista Nicolas Zhang ya ce kungiyar takan halarci manyan tarurruka na ‘yanjarida a kasashen ketare tare da kulla kawance da su domin yaukaka zumuncin aiki.
Kamar yadda wasu bayanai daga cikin wani littafi da kungiyar ta raba wa tawagarmu game da kafuwar gidajen yada labarai a kasar Sin, akwai ‘yanjarida a kasar Sin kimanin dubu dari biyu da ishirin da uku da dari tara da ishirin da biyar (223,925). Daga cikin adadin, bangaren jarida yana da ma’aikata dubu tamanin da hudu da dari da talatin (84,130), mujallu da muqalu na musamman suna da ma’aikata dubu shida da bakwai (6,007), bangaren kamfanin dillancin labaru na da ma’aikata dubu biyu da dari takwas da daya (2,801), sai gidajen radiyo da talabijin da dakunan shirya fina-finai da ke da ma’aikata dubu dari da ishirin da tara da dari takwas da ishirin da tara (129,829), kana sashen shafukan yada labaru na intanet yana da ma’aikata dubu daya da dari da hamsin da takwas (1,158).
Daga cikin dukkan wadannan adadin maza suka fi yawa inda suke da fiye da kashi hamsin da biyu a cikin dari (52.45%) sai mata da ke da fiye da kashi arba’in da bakwai a cikin dari (47.55%).
Kungiyar ta daukacin ‘yanjaridun kasar Sin, ta kafa sashe na musamman da ke saurarar koke-koken ‘yanjarida a koyaushe tare da bude adireshin imail da samar da lamba ta musamman don sadarwa a tsakanin ‘yanjarida masu koke da kuma kungiyar. Kungiyar ta ce takan zurfafa bincike sosai tare da nuna goyon baya da neman biyan diyya ko matsawa a nemi gafarar duk wani danjarida da aka tauye ma sa hakki.
Ta buga misali da cewa, a shekarar 2016, akwai ‘yanjarida uku daga kafar yada labaru ta Lanzhou Morning Post da wasu biyu daga kafafen yada labarun Birnin Wuwei da jami’an tsaro suka damke, da wani danjarida na gidan radiyo da talabijin na Harbing da aka ci ma sa mutunci lokacin da yake daukan rahoto, sannan da wani danjaridan Mujallar West China Development da aka tauye ma sa ‘yancinsa na rayuwa, duk ta yi tsayuwar-daka tare da hukumomin kafafen yada labarunsu wajen bi musu hakki kamar yadda dokar kasar ta shimfida.
Ba wannan ba kadai, kungiyar ta ce tana kuma ba da tallafi ga ‘yanjarida mabukata wadanda suka gamu da ibtila’i yayin gudanar da aikace-aikacensu. Ta ce a shekarar 2015 ta tallafa wa ire-iren wadannan ‘yanjaridan da kudi sama da RMB dubu dari uku da sittin (360,000) wato kimanin Naira milyan ishirin da dubu dari da sittin (20,160,000). Bugu da kari, a shekarar 2016, ta sake ba da tallafin ga wasu ciki har da iyalan wadanda suka mutu a bakin aiki da kudi RMB dubu dari takwas da casa’in (890,000), wato kimanin Naira milyan arba’in da tara da dari takwas da arba’in (49,840,000).
Hakika bisa wannan namijin aiki da kungiyar ta daukacin ‘yanjaridan kasar Sin ke yi, za a iya cewa daga kafuwarta zuwa yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu.


Advertisement
Click to comment

labarai