Connect with us

LABARAI

Tawagar Bankin Duniya Sun Iso Nijeriya Ba Tare Da Yin Magana Kan Bashin El-Rufai Ba

Published

on


A na sa ran tawagar bankin duniya (World Bank) da suka hada da daraktoci 10 zasu iso Nijeriya ranar Laraba domin tataunawa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ministan kudi Kemi Adeosun da kuma wasu gwamnonin jihohi a kan wasu aiyukan da bankin ke gudanarwa  a wasu sassan kasar nan.

Sanarwa da ta fito daga ofishin mataimakin shugaban kasa ya nuna cewa, takagar zasu tattauna aiyukan da bankin ke gudanarwa a sassan kasar nan tare da mataimakin shugaban kasa da wasu gwamnonin jihohi.

Jami’an bankin za kuma su hadu da masu manyan kanfanoni masu zaman kansu Legas, za kuma su ziyarci aiyukan da LAPO Microfinance ke gudanarwa a Legas da kuma aikin wuta na Azura Power Plant a jihar Edo, amma tawagar sun ki cewa komai a kan shirin karbar bashin Dala Miliyan 350 da gwamman jiharb Kaduna Nasir El-Rufai ya nema amma wasu ‘yan majalisar dattijai daga jihar suka ki amincea da shi.

Bayanan da ‘yan jarida suka samu ya nuna cewar, ziyarar zai tattauna kalubalen da gwamnatin tarayya dana jihohi ke fuskanta wajen aiwatar da aiyukan da bankin duniyan ke gudanarwa da kuma yadda za a karfafa gabatar da mulki na gari a cikin al’umma. Taron zai kuma karfafa burin bankin duniyan a kasashe da kuma tallafa musu a inda ya dace.


Advertisement
Click to comment

labarai