Connect with us

LABARAI

Shari’ar Bafarawa Da EFCC: Babbar Kotun Sakkwato Za Ta Sa Ranar Yanke Hukunci

Published

on


Babbar Kotun Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Mai Shari’a Bello Abbas za ta yanke hukunci kan shari’ar da ke gudana a tsakanin Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa da Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) a ranar 4 ga watan Yuli 2018 wadda aka kwashe tsayin shekaru tara a na fafatawa.

Wadanda ake karar Bafarawa tare da su sune kaninsa Nasiru Bafarawa da kamfunan Beedash Nigeria Limited, NasdalBaf Nigeria Limited da kuma fitaccen dan siyasa Salihu Mai Buhu Gummi kan zargin aikata laifuka 33.

Zarge-zargen da ake yi wa Bafarawa da mutanen hudu sun hada da siyar da hannayen jarin Gwamnati ba bisa ka’ida ba da almubazzaranci da kudaden al’umma da kuma zamba cikin aminci daga 2003 zuwa 2007 lokacin da yake a matsayin Gwamna.

Mai Shari’a, Bello Abbas ya daga shari’ar ne zuwa ranar 4 ga watan Yuli domin yanke hukunci bayan duka bangarorin biyu sun gabatar da bayanai tare da rufe bayanan su na kariya. Alkalin ya gode masu kan hakurin da suka nuna tare da tabbatar masu cewar kotu za ta yi masu adalci.

Tun da fari a ranar Talata, Lauyan EFCC, Mista Jacob Ochidi ya bayyana cewar sun yi kokarin tabbatar da zargin laifuka 11 da aka bayyana. Haka ma Lauyan ya roki kotun da ta hukunta wadanda ake zargi a bisa ga bayanai da shaidun da aka gabatarwa kotu.

A bayanansa Lauya mai kariya, Lateef Fagbemi (SAN) ya bayyana cewar masu kara sun yi fatali da tuhuma 11 haka kuma sauran abubuwan ba su wajaba ba a kokarin tabbatar da sauran zarge-zarge 22 wadanda ba su wadatar ba wajen hukunta wadanda ake zargi domin doka ta ayyana cewar wajibi ne a tabbatar da zargi yadda ya kamata.

Don haka Lauyan ya bukaci Kotun da ta sallami wadanda ake tuhumar tare da wanke su ga tuhumar domin masu kara sun kasa tabbatar da zargin da suke yi wa masu kariya.

Barista Lateef Fagbemi SAN ya kuma bayyana cewar ya kamata a bayyana Bafarawa a matsayin nagartaccen mutum mai gaskiya da amana wanda ya gabatar da korafi yanzu kuma ya dawo wanda ake zargi domin a cewarsa shine tun da farko ya gabatar da koke ga Hukumar EFCC a 2006.


Advertisement
Click to comment

labarai