Connect with us

LABARAI

Saraki Ya Ziyarci Sabon Ofishin Hukumar EFCC

Published

on


Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya kai ziyara sabon babban ofishin hukumar EFCC, inda ya yi alkawarin bayar da taimako na musamman domin karfafa ma’aikatu da hukumomi a kasar nan.

Sanarwa da jami’in watsa labaran shugaban majalisar, Mista Sanni Onogu, ya ce, Saraki ya bayyana matukar jin dadinsa a bisa ingancin aikin da aka gudanar na gina sabon babban ofishin hukumar EFCC, musassaman ganin cewa, dan NIjeriya ne ya zana ginin gaba daya.

Ya ce, ziyarar nasa ya zama dole ne saboda ganin mahimmancin hukumar ga majalisar kasa da kuma gudummawar da majalisar ta bayar wajen kafuwar hukumar.

Da yake tattaunawa bayan zagaye ginin, ya ce, karfafa hukumar zai yi matukar taimakon Nijeriya a kokarin data keyi na yaki da cin hanci da rashawa.

“Idan ka lura da wasu gine gine a garin Abuja ban yi tsammanin a kwai aikin daya samu kulawa na kudi daga majalisar kasa kamar wannan ginin ba, wannan yana wara nuna irin kokarin majalisar ne na bayar da gudunmawa a inda ya dace”

“In ka kara lura da abin da aka cimma a cikin shekaru 2 da rabi na gina wannan katafaren ginin, lalai wannan nasara mai dimbin yawa”

“Duk da banbance banbancen da muke das hi, daga karshe dole mu hada hannu mu samar da ma’aikatu da hukumomi karfarfa, za kuma mu ci gaba irin wannan aikin” inji shi.

Ya kara da cewa, dole a ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa in har muna son samar wa al’ummu masu zuwa rayuwa na gari, domin babu rayuwar da za a samu ana gari ba tare da anyi yaki da cin hanci da rashawa ba.

“Kamar yadda nake cewa a kowanne lokaci, a ci gaba yaki da cin hanci da rashawa dole mu karfafa hukomin da suke wannan aiki saboda duk wanda yazo daga baya zai fahinci irin kokarin da aka yin a karfafa hukumomin”

Da aka tambaye shi, abin da kammala wannan aiki ke nufi in aka kwatanta da ci gaba da gudanar da mulkin gwamnati, sai ya ce, “Abin daya sa ken an nake cewa, lamarin ba wai na mutum daya bane , lamarin gaba daya na ci gaban kasa ne, wannan aikin kuma abin da yake nunawa kenan.

“Aikin ya samu albarkan shugabannin hukumar guda 3, kuma kowanne a cikinsu ya dauki aikin a matsayin nasa, ba wai ya ce, tunda bashi ya fara ba bto zai kawao wa aikin cikas, dukkansu sun dauki aikin kamar nasu, hakan kuma ya taimaka wajen kammala aikin gaba daya.

“Ina da yakinin cewa, wannan wani abu ne da zamu yi alfahari da shi a shekaru masu yawa nan gaba.

Majalisar kasa ta dan samu takaddama da sashin shugaban kasa game da batun amincewa da shugabancin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu inda suka yi fatali da bukatar shugaba buhari na a amince da Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar.

Sau biyu shugaba Buhari na gabatar da Ibrahim Magu a dukkan lokuttan kuma majalisar kasar na fatali da sunan Ibrahim Magu din.

Shugaban majalisar dattijan ya ce, ba wai suna da wani bita da kulli a kan Ibrahim Magu bane, amma sun ki amince das hi ne a bisa rahoton da hukumar leken asiri na kasa SSS, kuma an gudabar da taron tantance shi ne kai tsaye a kafafen watsa labarai inda dukkan ‘yan Nijeriya suka kalla. Ya ce, kin amincewa da sunan Magu abu ne da zai taimaki harkar dimokraddiya.

A nasa jawabin, shugaban hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu, ya gode wa shugaban majalisar a bisa goyon bayan da suka bai wa hukumar musamman na ganin an kamala katafaren ginin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai