Connect with us

LABARAI

Sandar Majalisa: An Kafa Kwamitin Da Za Su Yi Bincike

Published

on


Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, a ranar Talata ya kaddamar da wani kwamitin hadin gwiwa da Majalisar Wakilai da zai binciki harin da aka kawo ma Majalisar ranar 18 ga watan Afrilu wanda ya kai ga sace sandar ikon Majalisar.

Maharan sun tsere ne daga farfajiyar Majalisar tare da sandar a cikin wani jerin motoci hudu.

Akwai rahotannin da ke nu na hadin baki da wani sashe na jami’an tsaro kan kawo harin da sace sandar.

Bayan ‘yan kwanaki, sai ‘yan sanda suka ce sun kama mutane shida da suke tuhuma, sama da wata guda kenan su na ta ci gaba da tuhumar su, ba tare da sun gurfanar da kowa ba, duk da bayyanan hotunan ainihin ~arayin a shafin sadarwa na, PREMIUM TIMES, da ma wasu shafukan.

A maganan da ya yi ranar Talata, Saraki, ya kwatanta abin da ya farun a ranar 18 ga watan Afrilu a matsayin daya daga cikin bakaken ranakun Dimokuradiyya a kasarnan.

Ya kuma sha alwashin Majalisar za ta yi duk abin da ya dace na ganin ta maido da kimar ta, ya ce ba za a lamunci keta hurumin babbar Majalisar ba.

“An ta yadawa a wurare masu yawa cewa, wadannan ‘yan daban da yaran su, wani Sanata ne mai ci a halin yanzun ya jagorance su, wannan babban abin kunya ne da mamaki.

“Mun daukar wa kanmu, ba wannan lokacin ba kadai, har ma lokutan wadanda za su gaje mu, za mu magance shigen aukuwan wadannan lamurran, mu dawo ma da Majalisar nan kimar ta. Ya zama tilas mu yi hakan. Ba za mu lamunta hakan ya sake aukuwa ba. Duk wanda ke da hannu wajen aikata wannan babban laifin, sai an hukunta shi, in ji Bukola.

Saraki ya fada a ranar Talata cewa, wani binciken mai kama da wannan da hukumar kula da Majalisar ta yi, ya kammala aikin sa, ya ma mika sakamakon binciken na shi. Yanzun ana sa ran sabon kwamitin da Majalisar ta kafa ne zai nazarci sakamakon binciken.

Wakilan kwamitin sun hada da, Shugaban masu rinjaye, Ahmed Lawan, Sanatoci, Abu Ibrahim, John Owan Enoh, Shehu sani, Samuel Anyanwu, Suleiman Hunkuyi, Baba Kaka Garbai da Binta Garba. Mataimakin shugaban masu rinjayen Majalisar, Bala Ibn Na’Allah, ne zai shugabanci kwamitin.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai