Connect with us

LABARAI

Rasuwar Khalifa Isyaka Rabi’u Babban Rashi Ne Ga Nijeriya, Inji Shaikh Dahiru Bauchi

Published

on


Fitaccen Malamin Darikar Tijjaniyya a Nijeriya, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya nuna jimaminsa gaya a bisa rasuwar Khalifa Isyaka Rabi’u wanda kuma babban Malamin addini ne, kuma dan darikar ta Tijjaniya, wanda ya rasu a ranar Talata a kasar London a yayin da ke amsar kulawar likitoci.

Sheikh Dahiru Bauchi wanda yake mika sakon ta’aziyyarsa a daren ranar da marigayin ya rasu a gidansa da ke Bauchi, ya misalta marigayin a matsayin wani jajirtaccen da ya yi amfani da iliminsa da kuma dukiyarsa wajen ci gaban addinin Islama musamma a Nijeriya da Nahiyar Afrika.

Shaikh Bauchi ya bayyana cewar a gefe guda marigayin Mahaddaci ne kuma hamshakin mai kudi, wanda hakan ta bashi zarafin taimakon addinin Musulunci ta fuskacin yada shi, gina masallatayya, da kuma makarantun domin koyar da addinin na Islama a lokacin da ke raye.

Ta bakinsa Shaikh Dahiru; “Na samu Labari mai matukar tayar da hankali na rasuwar Malam Isyaka Rabi’u wanda ya rasu a kasar London. Allah ya jikansa, Allah ya yi masa gafara,”

Ya kara da cewa, Nijeritya baki dayanta ne ta yi babban rashi ba ma kawai su ‘yan darika kadai ba, “Hakika an yi babban rashi a Nijeriya; mu Mahaddata mun yi rashin dan uwanmu Mahaddashin Alkur’ani, mu ‘yan Tijjaniyya mun yi babban rashin dan uwanmu dan Tijjaniyya, masu kudi sun yi rashin dan uwansu mai kudi. Allah ya gafarta masa ya kuma jikansa,” In ji Bauchi.

Da yake bayani kan irin gagarumar gudunmawar da Khalifa Isyaka Rabi’u ya bayar

wajen daukaka darajar addinin Islama gami da koyar da sahihin koyarwar Manzon Allah, Dahiru Bauchi ya bayyana sa a matsayin wani jan gwarzon da ya yi kokari sosai, “Ya gina massalatai da yawan gaske, ya kuma gina makarantu da dama, ya taimaki miskinai da yawa, Allah ya amshi kyawawan aiyukansa ya yafe masa dukkanin kurakuransa,” A cewar shi.

Shehu Dahiru Bauchi, ya kuma yi tsokaci kan girman marigayin a cikin Darikar Tijjaniyya, inda ya misalta sa da cewar wani babban mai hidima wanda matsayinsa ta kai lamba daya, “Shekarun da, da suka wuce gabanin fitowar rigimar Khalifanci da ake yi, muna alfahari da shi cewa Nijeriya ba mu da abun alfahari kamar sa. Shi ne zai zauna ya yi darasu daga la’asar, idan ya yi sallar magriba ya bude wazifa da safe kuma ya fita zuwa kanti, babu mai yin wannan sai shi,”

Sai ya yi addu’ar Allah ya amshi uzurinsa ya gafarta mashi, “Allah ya gafarta masa, ya yaye masa dukkanin zunubansa, ya raya yaransa a cikin addini da mutunci, Allah ya baiwa mutanemu hakurin jure wannan rashin,”

Dahiru Bauchi ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Sarkin Kano, Malaman Darika, Shehunani, Zuri’arsa, Gwamnatin Kano da dukkanin wadanda abun ya shafa “Musamman mu kanmu ‘yan Tijjaniyya. Ina kuma mika sakon ta’aziyya wa mutanenmu na Kaulaha da mutanemu da suka saba da shi. Innalillahi Wa inna’illahir raji’un, Allah ya jikansa da jinkansa,”.

Shaikh Dahiru Bauchi ya kuma yi amfani da wanna damar ya bayyana wasu abubuwan da suka faru a tsakaninsu da marigayin a lokacin da ke raye, inda ya yi misalinsa da cewar mutum ne mai hakuri da kawaici “Shi dan uwana ne wanda ban da kamarsa a Nijeriya,” kamar yadda ya fadi.

Ya kuma kara da cewa, “Duk wanda Allah ya bashi Alkur’ani Allah ya yi masa komai, duk wanda ya samu kur’ani ya gode wa Allah domin Allah ya bashi komai fiye da komai,” a cewar Dahiru Bauchi.

LEADERSHI A YAU dai ta labarto a jiya cewar Khalifa Isyaka ya rasuwa yana dan shekaru 90 a duniya. Marigayin ya kasance daya daga cikin mashahuran Malamai, kuma babban dan Kasuwa wanda ya shahara a tsakankanin 1970s da 1980s.

Kafin rasuwarsa, Khalifa Isyaka Rabiu ya kasance daya daga cikin jagororin Darikar  Tijjaniya a Nijeriya.

Khalifa Rabiu ya rasu ne Birnin Landan ya kuma rasu ya bar mata da ‘ya’ya da dama, wanda a cikin ‘ya’yan nasa akwai Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu.

An haifi Khalifa Isyaka Rabiu a gidan Malam Muhammadu Rabiu Dan Tinki, wani shahararren masanin Al-kur’ani a garin Bichi ta Jihar Kano.

Sannan kuma a marigayin yayi karatun addini; Al-kur’ani da larabci a makarantar mahaifinsa daga shekarar 1936 zuwa 1942. Sannan kuma marigayin ya je garin Maiduguri na Jihar Borno inda ya karo ilimin addini. A farkon 1950 lokacin Khalifa Isyaka Rabiu na koyarwa, sai kuma ya hada da kasuwanci, inda ya assasa  ‘Isyaka Rabiu & Sons’ a shekarar 1952.


Advertisement
Click to comment

labarai