Connect with us

LABARAI

Mun Kama Masu Kai Wa Makasa Bindigogi A Jihohin Benuwe Da Taraba –’Yan Sanda

Published

on


A ranar Talata ne ‘yan sanda suka yi holin wadansu mutane da ake zargi da kawo ma masu kashe-kashe al’ummu a Jihohin Benuwe da Taraba, makamai.

Cikin sanarwar da Kakakin rundunar ‘yan sandan, Jimoh Moshood, ya fitar a ranar Talata da yamma, ya lissafta sunayen mutanan da aka kama da kuma makaman da aka kama su da su.

1.Sabuwar dubarar da rundunar ‘yan sanda ta fito da ita domin dakatar da kashe-kashen ‘yan Nijeriya da kuma dakile hanyoyin watsuwan makamai a cikin kasa, musamman a Jihohin tsakiyar Arewa, su ne ke haifar da da mai ido. Rundunonin da Shugaban ‘yan sanda ya kafa da suke yin aiki a Jihohin Benuwe, Nassarawa da Taraba, a makwanni biyu da suka shige sun kama mutane 11, sun kuma gano bindigogin AK 47 guda 10 da wasu makaman da harsasai a tare da su.

 1. A tuhumomi biyu na farko, mutanan da ake tuhuma duk sun amsa cewa, su ne suke kaiwa makasan, ‘yan fashi, makiyaya da manoma da sauran masu aikata muggan laifuka bindigogin AK 47 da sauran makamai da harsasai a Jihohin Benuwe da Taraba.
 2. Wanda ake tuhuma na farko, Morris Ashwe, 36 dan garin Mbajima, da ke karamar hukumar Katsina Ala ta Jihar Benuwe, ya amsa laifi, ya kuma yarda yana kaiwa fitaccen jagoran kungiyar nan masu kai hare-haren kabilanci, mai kashe mutane, mai sace mutane, Terwase Akwaza, wanda aka fi da kira, Ghana, wanda muka fi da nema ruwa a jallo, wanda a baya mun bayar da sanarwar neman sa, kan tuhumomin kashe mutane masu yawa da ~arnatar da dukiyoyin milyoyin Naira, a garuruwan ZakiBiam ta Jihar Benuwe, ranar 20 ga watan Maris 2017, da ma wasu manyan laifukan da suka shafi kisan kai, cinna gobara da hada baki a aikata laifi da kashe Mista Denen Igbana, babban masahawarcin gwamnan Jihar Benuwe kan harkar tsaro.
 3. A tuhuma ta biyu, duk mutane ukun da ake tuhuma, ma su suna, Kabiru Idris, Miracle Emmanuel da Husseini Safiyanu, an kama su ne a Jihar Taraba, an kama su da bindigogin AK47 guda biyar, da kwanson harsasan AK47 guda 13, da harsasi 83 na AK 47. Sun kuma amsa cewa su na kaiwa dakarun bangar kabilanci bindigogin AK 47 da sauran makamai a Jihohin Taraba da Benuwe, wadanda suka ce sune ke kai hare-hare da kashe mutane a kauyakun na Jihohin Benuwe da Taraba.
 4. Tuhuma ta uku, ta kumshi masu garkuwa da mutane ne su bakwai. An kama su ne a lokacin da suke tafiya domin sato wani babban mutum a garin Makurdi. an kuma samu bindigogi samfurin Beretta guda biyu a tare da su. Sun amsa sune ke aikata ayyukan satan mutane a Jihohin Benuwe da Taraba da kuma wasu sassa na Jihar Nassarawa, a can baya.
 5. Ana ci gaba da zafafa bincike domin gano sauran wadanda ake zargin. Da zaran an kammala bincike duk za a gabatar da su a Kotu.
 6. Kawo karin rundunonin ‘Yan sandan kwantar da tarzoma 15 da aka yi domin kara karfafa tsaro a Jihar ta Benuwe, ya samar da zaman lafiya a Jihar.
 7. Rundunar ‘yan sanda tana tabbatar wa da al’ummun Jihar Benuwe da sauran Jihohin da a baya ke fama da matsalar tsaro, aniyar ta na tabbatar da zaman lafiya a Jihohin na su.

Sunayen Wadanda Ake TuhumanTuhuma ta farko: Dillalan Bindigogi

 1. Morris Ashwe 36, mutumin garin, Mbajima da ke karamar hukumar Katsina Ala, ta Jihar Benuwe (Yana ma Terwase Akwaza, da aka fi sani da, Ghana, aiki ne).

Abubuwan da aka samu a tare da shi sune:

 1. Bindigar AK47 guda biyar,
 2. Kullin harsasan AK 47 guda 238

iii.      Kanista guda 40

 1. Harsasan bindigar LAR guda 79

Tuhuma Ta Biyu: Dillalan Bindigogi

 1. Kabiru Idris, 43, an kama shi ne a Takum, ta Jihar Taraba.
 2. Miracle Emmanuel, 27, babban mai laifi jagoran tawagar, mutumin Jihar Anambra.

iii.      Hussaini Safiyanu, Mutumin Jihar Taraba, babban mai laifi.

Abubuwan da aka gano a hannun su sune:

 1. Bindigogin AK 47 guda biyar
 2. Kwanson harsasan AK47 guda 13

iii.      Kullin harsasan AK47 guda 83

Tuhuma ta uku: Masu garkuwa da mutane da ‘Yan fashi da makami

 1. Emmanuel Ushehemba Kwembe, 28, mutumin karamar hukumar Ushongo ta Jihar Benue.
 2. Sekad Uber 28, mutumin karamar hukumar Koshisha, ta Jihar Benuwe.

iii.      Ordure Fada 22, Ordure Fada 22, mutumin karamar hukumar Kwande, ta Jihar Benuwe.

 1. Stephen Jirgba 18, mutumin karamar hukumar Bande, ta Jihar Benuwe.
 2. Peter Lorham 24, mutumin karamar hukumar Kinshisha, ta Jihar Benuwe.
 3. Achir Gabriel 30, mutumin karamar hukumar Ushongo, ta Jihar Benuwe.

bii.     Lorhemen Akwambe 35, mutumin karamar hukumar Guma, ta Jihar Benuwe.

Kayan da aka kama su da su:

 1. Kananan Bindigogi samfurin Beretta guda biyu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai