Connect with us

LABARAI

Matan Gwamnoni Sun Nuna Damuwa Kan Yawaitar Shaye-shaye A Arewa

Published

on


A bisa ga yawaitar shaye-shaye da illar da hakan ke haifarwa ga mata da matasa a Yankin Arewa; Kungiyar Matan Gwamnonin Arewa a ranar Talata sun hadu a Sakkawato domin gudanar da taron kwanaki biyu kan bahaguwar matsalar da hanyoyin magance ta.

A jawabin ta Shugabar Kungiyar Matan Gwamnonin Arewa kuma Uwar Gidsn Gwamnan Bauchi, Hajiya Hadiza M. A Abubakar ta bayyana cewar illar shaye-shaye ya jefa yankin Arewa cikin wani yanayi musamman bisa ga matukar lahanin da yawaitar shaye-shayen yake da shi ga rayuwar mata.

Ta ce “Kalubalen namu ne bakidaya kuma ya zama wajibi mu himmatu ga wannan illar da samar da hanyoyin shawo kan ta. Abin damuwa ne kwarai jin cewar mata ne ke da kaso mafi yawa na mashaya wanda kuma idan ba a dauki mataki ba zai zama illa ga makomar matasa masu tasowa.” Ta bayyana.

A taron wanda aka gudanar a Fadar Gwamnatin Sakkwato ta kara da cewar “A matsayin mu na iyaye mata kuma masu tarbiyar halayen ‘ya’yan mu ya zama wajibi mu basu cikakkiyar kulawa mai kyau maimakon tarbiyar maras kyau wadda za ta zama hadari gare su.”

Uwar Gidan Gwamnan ta Bauchi ta bukaci a kara kafa Cibiyoyin Gyara Halayen Mata tana cewar sun riga sun kaddamar da wata cibiya a Kogi a yanzu kuma za su kaddamar da wata a Sakkwato.

A jawabin ta na maraba, Uwar Gidan Gwamnan Sakkwato, Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal ta bayyana cewar yawaitar shaye-shayen da mata ke yi a Arewa abin damuwa ne kwarai ainun wanda ke bukatar a taka masa burki.

Ta bayyana cewar babban nauyi da kuma manyan manufofi da kudurorin kungiyar sune taimakawa wajen magance matsalolin da mata da kananan yara ke fuskanta tare da inganta rayuwar mata.

Mariya Tambuwal ta yi kira ga Malaman makarantu da a bisa ga matukar muhimmanci su rika bayar da kulawa ga rayuwar dalibai tare da kai rahoton shaye-shaye ga hukumomin makaranta domin daukar mataki.

“A sakonsa yayin bude taron, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana taron a matsayin wanda aka kira a lokaci mafi dacewa tare da kira ga Matan Gwamnoni da su jajirce wajen shawo kan kalubalen da yankin ke fuskanta na yawaitar shaye-shaye.

Ya ce “Ina fatar al’ummar wannan yankin za su tashi tsaye domin shawo kan wadannan matsalolin da yankin ke fuskanta.” In ji Gwamnan.

 


Advertisement
Click to comment

labarai