Connect with us

LABARAI

Malamai Dubu 61,000 Kadai Ake Da Su A Jami’o’in Nijeriya 152 –Shugaban NUC

Published

on


Babban Sakataren Hukumar kula da Jami’o’i ta kasa NUC, Abubakar Rasheed, ya bayyana cewa, baki daya-kwata, Malamai dubu 61,000, ne suke karantarwa a Jami’o’i 164 na kasarnan, masu dauke da dalibai milyan 1.96,  a yanzun haka.

Ya kuma bayyana cewa, rashin Shugabanci nagari ne babban matsalan da ke hana Jam’o’in na Nijeriya samun yanayin koyarwar da ta dace.

Rasheed, yana wannan maganan ne ranar Talata a Abuja, wajen wani taron yini biyu na hukumar gudanar da Jami’o’in ta kasa, taken taron dai shi ne, “Elements of Statutory Gobernance, Procurement da Financial Accounting in Nigerian Unibersities.”

Ya nanata cewa, ba ta yadda za a sami koyarwar da ta dace a Jami’o’in namu, tare da kasancewar Malamai 61,000 ne kacal suke karantar da kusan dalibai milyan biyu.

Kan haka, sai ya yi nu ni da cewa, gwamnatoci ne kashin bayan ilimin manyan makarantu a duk duniya, amma a cewar sa, rashin jagoranci da shugabanci nagari ne suka taru suka hana Jami’o’in namu kaiwa ga sa’o’in su, ta hanyar koyarwa, bincike da ayyukan al’umma.

Ya nu na juyayin sa kan tsarin shugabancin da ke cikin Jam’o’in kasarnan, wadanda suke nu na damuwa kwarai sabili da rashin shugabanci nagari, ayyukan cuwa-cuwa, rigingimun da za a iya kauce masu, rashin yin abubuwan da suka dace, zaunannan kidahumanci, rashin samun koyarwa nagari da ma rashin samun wurin da ya dace da koyarwar.

Ya kara da cewa, da yawa daga cikin matsalolin shugabanci a Jami’o’in namu, sun samo asali ne daga rigingimun shugabanci da jagoranci.

Ya ce, sabili da irin wadannan matsalolin ne da wasu kalubalen da ke fuskantar Jami’o’in, hukumar ta NUC, tare da hadin gwiwan kwamitin mataimakan shugabannin Jami’o’in na kasa da kuma kwamitin Farfesoshi, suka yanke shawarar shirya wa shugabannin hukumomin zartaswan Jami’o’in, mataimakan su, Magatakardan Jami’o’in da masu lura da harkokin kudi na dukkanin Jami’o’in gwamnatin tarayya 42 wannan taron kara wa juna sanin.

Shugaban hukumar ta NUC, ya ce, ya yi farin cikin zuwan taron a daidai lokacin da hukumar na shi ke daukan wasu kwararan matakai na farfado da Jami’o’in na Nijeriya.

Ya ce, ya kamata mu ~ullo da wata sabuwar hanyar da za ta magance wadannan matsalolin, yana cewa, “Za mu iya kara yawan daliban Jami’o’in ne da kashi 50 nan da shekaru biyar. A maimakon milyan biyu, mu na sa ran su zama milyan uku ne a badi?

“Na ji dadin kasantuwan babban Sakataren gidauniyar ilimin manyan makarantu, Abdullahi Baffa, yana zaune a wannan wajen, Daya zuwa biyu, na manyan matsalolin Jami’o’in Njeriya su ne rashin wuri, saboda matsalan kayan aiki da kuma rashin yawan malaman da suka cancanta, wadanda wadannan su ne babban sashen da hukumar ta, TETFund, take mayar da hankali a kansu.

“Muna da kimanin dalibai milyan 1.96 a cikin Jami’o’inmu, da malamai dubu 61,000 kacal, wanda hakan sam bai isa ba.

“A Jami’ar Odford, su na da kimanin dalibai dubu 17,000 ne, tare da kimanin malamai 13,000 masu koyarwa a Jami’ar. Wannan shi ya sanya Jami’ar ke kaiwa ga abin da ake bukata daga gare ta, Farfesa daya ga dukkanin dalibai biyu, su na kuma zama tare a duk mako tsawon zaman su a Jami’ar.

“A can muna da malamai dubu 13 ne masu karantar da dalibai dubu 17, a nan kuma, muna da malamai dubu 61 ne, masu karantar da dalibai milyan biyu. Duk kokarin ma da muke yanzun shi ne na yadda za mu iya daukan nauyin malamai dubu 40 nan da shekaru biyar,” in ji Rasheed.

Farfesa Peter Okebukola, ya gabatar da wasu takardu biyu a wajen taron, kan matsayin Jami’o’in namu, da suka hada da, “The State of Nigeria Unibersity System 2017” da kuma, ‘Digest on Nigerian Unibersity System.’

Shugaban hukumar zartaswa na hukumar ta NUC, Farfesa Ayo Banjo, cewa ya yi, burin Jami’o’i a duk duniya shi ne su kai ga manjufar kafa su, sai ya ce, amma yawancin daliban da Jami’o’in na Nijeriya ke kyankyashewa akwai ayar tambaya a kansu.

Ya ce, duk dalibin da ya kammala karatun sa na Jami’a, amma bai iya tunani yadda ya dace, to bai cancanci a ba shi takardar shaidar kammala karatun digiri ba.

Ya ce, ana cewa ba wata Jami’a a Nijeriya da za ta iya kasancewa cikin jerin Jami’o’i 500 da ke sahun gaba a duniya, sai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran masu mallakan Jami’o’in da su baiwa Jami’o’in kudade sosai domin su gudanar da ayyukan su yadda ya dace.

Mista Banjo, ya bayar da shawarar a rika biyan kudin makaranta, domin a sami damar gudanar da Jami’o’in yadda ya dace.


Advertisement
Click to comment

labarai