Connect with us

LABARAI

Majalisa Ta Bukaci FRSC Ta Daina Ba Jahilai Lasisin Tuki

Published

on


Majalisar dattijai ta bukaci hukumomin gwamnati dake da alhakin tabbatar da tsaron lafiyar hanyoyinmu dasu tabbatar da direbobi sun mallaki kwarewar daya kamata tare da kuma sun iya karatu da rubutu da yaren Ingilishi.

Majalisar ta kuma bukaci hukumomin daya kamata su tabbatar da ana bai wa masu bukatar lasisin tuki darasi akan alamomin hanyoyi da sauran darussan da zasu taimaka wa direba sanin dokokin hanya domin kare hatsaurra a kan hanyoyinmu.

Wannan shawarar ya biyo bayan wani kudurine da Sanata Umaru Kurfi (APC Katsina ta Tsakiya) ya gabatar a zaman majalisar mai taken, “Need to address the low lebel of literacy amongst dribers in Nigeria”.

Da yake gabatar da bayani a kan kudurin, Sanata Kurfi, ya lura cewa, “yawancin direbobin da ake daika a hukumomin gwamnati da kanfanoni masu zaman kansu basu da cikakken kwarewar daya kamata na aikin direba”

“yawancin su karatun firamare kawai suka kamala a rayuwarsu, zaka ti mamakin cewa da yawa a cikinsu basi iya karatu da rubutu ba” inji shi.

Ya kuma lura da cewa, “wannan lamarin ya haifar da mnatsaloli mai dimbin yawa tare da aukar da hatsurra a kan hanyoyimu saboda jahilicin dake tatare da direbobi, irn wadannan direbobi basu da ilimin sanin alamomin hanyan da zai taikamam musu wajen fahintar amfani da hanya” Sanata Kurfi ya ce, majalisar dattijai ta damu da cewa, wasu direbobin na fuskantar matsala wajen banbance tsakanin takardun motocinsu ya kuma lura da cewa, “Wannan ne ya haifar da fadawa takardun bogi a yayin da direbobi suka je canja takardun motarsu day a kare aiki”.

“WAyan hatsarin da mashina ke haifarwa a yan shekarun nan yana matukar tayar da hankula, matsala amfani da masjina ya samnya wasu birane a kasar nan sun haramta zirga zirga dad a shi a cikin biranensu saboda matsalolin da suke haifarwa”

“Abin lura kuma shi ne wayancin masu amfani da mashinan yara ne kanana wanda shekarunsu ya gaza 18 a duniya, basu da cukakken ilimin dokokin hanya da yadda zasu yi amfani dasu.” Inji shi.

A nasa gudumawar Sanata Aliyu Sabi Abdullahi (APC Neja ta Arewa) ya karfafa bukatar mahimmantar da lamarin ne saboda yawan motoci dake amfani da hanyoyin Nijeriya hakan zai yi matukar ceto rayuka da dukiyoyin dake salwanta a kullum a kan hanyoyinmu.

Ya ce, tuki ya zama aikin kowa a kasar nan a halin yanzu, “Hakan na faruwa ne saboda har yabzu babu wanu direba da aka hukuntab da laifin kisa duk da gangancin da direbobin keyi a han hanyoyinmu koda kuwa direba ya yi sanadiyar rasa rayukan iyalai 25 saboda ganganci da rashin sanin dokokin tuki”.

Haka kuma, a nasa tsokacin, Sanata Philip Gyunka (PDP Nasarawa ta Arewa) ya bukaci samar kudade na musamman domin hurar da direbobi saboda a tsirar da rayukan jama’a a kasar nan.

Ya ce, “Ya wancin hadurran da ake samu a kasar nan ganganci ke aukar dasu, a wasu lokuttan kuma durebobin ma basu san cikakken hakkokinsu ba ko kuma basu san abin da zasu yi ba a da kuma lokacin da zasu yi shi ba”.

Nasa tsokacin, shugaban majakisar dattijan Dakta Bukola Saraki, ya bukaci hukumomin da suka kamata a bangaren sifiri dasu fuskanci aiykansu yadda ya kamata su kuma tabbatar da sai wanda ya cancanta ne kawai zasu ba lasisi saboda tsirar da rayukan jama’a a kan hanyoyinmu.

Ya kuma umurci kwamitin majakisar dattijai akan sifiri dasu sanya ido sosai akan hukumomi kamr su FRSC domin tabbatarb da suna aikimsu yadda ya kamata.

 


Advertisement
Click to comment

labarai